Jirgin yaƙin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya kai sabon hari sansanin ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, a jihar Zamfara. Daily Trust ta ruwaito cewa ƙasurgumin ɗan ta’addan ya tsallake rijiya da baya a wani harin ruwan bama-bamai da sojoji suka kaddamar a gidansa ranar Asabar.
Wata majiya ya shaida mana cewa Jirgin ya sake koma wa wurin da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar yau Litinin, ya saki aƙalla bama-bamai guda biyu.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a kwanakin baya, gwamnatin Zamfara ta yi ikirarin cewa Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya da gwamnatin Matawalle ta zo da shi.
A halin yanzun, wasu ‘yan bindigan daji da ake kyautata zaton mayaƙan Bello Turji ne sun kai hari kan matafiya a babban titin Sakkwato zuwa Gusau, a ƙaramar hukumar Shinkafi.
Wani mazaunin garin Shinkafi, Murtala Wadatau, yace yan ta’addan sun tsohe hanya a Kwanar Badarawa da Birnin Yero da safiyar Litinin ɗin nan.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnati ta yi ikirarin cewa ta samu galaba kan taɓarɓarewar tsaron da aka sha fama da shi a sassan Najeriya. Gwamnatin ta bakin ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, tace duk da akwai sauran yaƙi, amma sojoji sun samu nasarori da dama kan ‘yan ta’adda.





