Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata mata a mota
Jirgin fasinja da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ya murkushe wata mata a mota har lahira a unguwar Kubwa da ke Abuja a yau Alhamis.
Rahotanni sun ce matar na kokarin tsallaka titin jirgin kasar ne da motarta, yayin da jirgin ke daf da ita, inda yai ciki da ita da misalin karfe 10:00 na safe.
Mai magana da yawun hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC), Mahmood Yakoob, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani.
Wani faifan bidiyo na wannan mummunan lamari da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna cewa jirgin ya murkushe wata bakar mota kirar Toyota Camry daga bangaren direban yayin da motar ke tsallaka titin jirgin, a yau Alhamis.
managarciya