Jihohin Da Ya Wajaba Tinubu Ya Ci Idan Yana Son Nasara A Zaben 2023

Jihohin Da Ya Wajaba Tinubu Ya Ci Idan Yana Son Nasara A Zaben 2023

Yayinda ake sauran kwanaki 177 zaben shugaban kasar Najeriya, wani rahoton jaridar ThisDay yayi hasashen jihohin da manyan takara ke bukatan ci. 

'Yan takaran sun hada da Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP da Rabi'u Musa Kwankwaso na NNPP. 

Rahoton ya yi bayanin jihohin da ya wajaba wanda ke son nasara cikin wadannan 'yan takara hudu ya samu  idan har yana non zama shugaban kasa. 
Game da Tinubu, rahoton ya lissafo jerin jihohin da ya wajaba ya samu kashi 60% da kuma 40% da kuma yiwuwan samun hakan. 

1 Lagos Ana Sa rai
 2 Ogun Ana Sa rai
 3 Ondo Ana Sa rai
 4 Oyo Da Yiwuwa (Sai Ya Dage)
 5 Osun Da Yiwuwa

 6 Ekiti Ana Sa rai
 7 Kano Da Yiwuwa (Kamar Wuya)
 8 Kaduna Da Yiwuwa (Sai Ya Dage)
 9 Katsina Da Yiwuwa (Sai Ya Dage)
 10 Zamfara Ana Sa rai
 11 Borno Ana Sa rai
 12 Yobe Ana Sa rai.
Jerin jihohin da ya wajaba Tinubu ya samu akalla 40% idan yana son zama shugaba 

Sokoto Ana Sa rai
 2 Kebbi Ana Sa rai
 3 Jigawa Da Yiwuwa
 4 Benue Da Yiwuwa (Kamar Wuya)
 5 Kogi Ana Sa rai
 6 Niger Ana Sa rai
 7 Kwara Da Yiwuwa
 8 Plateau Da Yiwuwa
 9 FCT Da Yiwuwa.
Abin lura: Mafi akasarin jihohin dake karkashin mulkin APC yanzu ake sa ran Tinubu zai samu rinjaye. 

Hakazalika Mafi akasarin jihohin dake karkashin mulkin PDP yanzu ake sa ran Tinubu sai ya yi da gaske.