Jihohin da Suka fi Dogaro ga Gwamnatin Tarayayya

Jihohin da Suka fi Dogaro ga Gwamnatin Tarayayya
 

Jihohi a Najeriya da dama na dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya domin yin wasu ayyuka da biyan albashi. 

Sai dai akwai jihohin da suka fi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayyar fiye da wasu a ɓangarorin kasar. 
Rahoton BudgIT ya fitar da wani bincike da ke nuna jihohin da suka fi dogaro da Gwamnatin Tarayya a kan wasu.
Jihar Bayelsa da ke da arzikin man fetur abin mamaki tafi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya a kasar da kaso 92.17 sai Akwa Ibom da kaso 86.29 da kuma Delta da kaso 83.89. 
Sai jihohin da suka fi karancin dogaro da kudin akwai Lagos da kaso 26.55 sai Ogun da kaso 31.95 sai kuma Zamfara da kaso 45. 
1. Jihar Taraba A cikin rahoton da aka fitar, jihar Taraba ta fi kowace jiha dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya a Arewacin kasar da kaso 81.89. Taraba da ke Arewa maso Gabas ta yi kaurin suna wurin arzikin noma da albarkatun kasa da ke ba da gudunmawa sosai wurin inganta tattalin arzikinta. 
2. Jihar Niger Niger ita ce jiha ta biyu a Arewa da tafi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya duk da albarkatun kasa da take takama da su. 
Niger da ke Arewa maso Tsakiyar Najeriya ta dogara da kudin Gwamnatin Tarayya da kaso 80.19. Sai dai a watan Yulin 2024, Gwamna Umaru Bago ya ce jihar ba ta dogara da kason Gwamnatin Tarayya ba, cewar Daily Post.
3. Jihar Benue Har ila yau, Benue da ke takama da arzikin noma saboda yalwar kasa ta kasance ta uku a Arewacin Najeriya da kaso 79.85. Jihar ita ma tana yankin Arewa ta Tsakiya da ta yi fice wurin samar da kaso mai yawa na abinci a fadin kasar baki daya. 
4. Jihar Bauchi jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas ta kasance ta hudu a Arewacin Najeriya da ta fi dogaro da kason da Gwamnatin Tarayya ke bata da kaso 75.33.
Duba da haka jaridar Punch ta tabbatar da cewa jihohi 24 a kasar sun dogara ne kacokan da kason Gwamnatin Tarayya domin biyan albashi.
5. Jihar Nasarawa Nasarawa ta zama ta biyar a Arewa wurin dogaro da kason Gwamnatin Tarayya da take rabawa kowane wata da kaso har 74.55, cewar The Guardian. 
Ita ma jihar ta fito daga yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya da ke makwabtaka da jihohin Benue da kuma Plateau. 
6. Jihar Gombe Jihar Gombe ta sanu wurin gudanar da harkokin kasuwanci inda ake ganin daga jihar Kano a harkar cinikayya sai ita a Arewa, cewar BusinessDay. 
Jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya tana dogaro da Gwamnatin Tarayya ne da kaso 72.29. 
7. Jihar Kano Kano ta kasance ta bakwai a jerin jihohin Arewa da suka fi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya da kaso 70.24. Jihar da ta yi fice fiye a Arewa game da harkokin kasuwanci ta fito ne daga Arewa maso Yammacin kasar.