Jihohi 8 da Peter Obi Zai  Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

Jihohi 8 da Peter Obi Zai  Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

 Jihohi 8 da Peter Obi Zai  Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

 
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo jihohin da ake tunanin jam’iyyar Labour Party za tayi wa Atiku Abubakar illa a zaben 2023. 1. Anambra Peter Obi zai iya samun gagarumar galaba a Anambra domin daga jihar ya fito, kuma ya yi gwamna sau biyu, yana da magoya-baya a yankin.
2. Abia Jihar Abia tana cikin jihohin PDP da suka samu sabani da Atiku Abubakar. Idan ba ayi sulhu ba, Peter Obi zai amfana da wannan baraka. 
3. Enugu Shi ma Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi yana tare da bangaren Nyesom Wike, zai yi wahala PDP ta maimaita nasarar 2019 a 2023 a Enugu. 
4. Ribas Gwamna Nyesom Wike ya sha alwashin yakar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa. Akwai yiwuwar hakan ya taimaki LP a zaben 2023.  
5. Kuros Ribas Jam’iyyar PDP ba ta da gwamna a Kuros Riba, kuma APC ba ta da karfi sosai. Akwai jiga-jigan siyasar jihar da za su taimakawa takarar Peter Obi. 6. Taraba Duk da karfin PDP, babu mamaki wasu yankunan jihar Taraba su zabi Peter Obi a badi, musamman yadda jam’iyyar LP ta ba John Ikenya takarar gwamna. 
7. Benuwai Alamu na kara nuna cewa Gwamna Samuel Ortom da manyan jihar Benuwai ba za su goyi bayan PDP a zaben shugaban kasa ba, watakila su zabi LP. 
8. Filato Ba abin mamaki ba ne tsohon gwamnan Anambra ya ba PDP har da APC mamaki a Filato. Ba wannan ne karon farko da LP ta ci zabe a jihar ba.