Jam’iyar NNPP ta jihar Jigawa a rasa wani jigo a tafiyar in da ya bayyana ficewarsa a wata takarda da ya aikewa jam’iyar a matakin mazabarsa ta Unguwar Gabas karamar hukumar Kazaure jihar Jigawa.
Bello Muhammad Zaki wanda yake tsohon mai magana da yawun tsohon Gwamnan jihar ne Badaru Abukakar ya shiga jam’iyar ADC.
“Bayan tuntubar iyali da dangi da magoya bayana da masu yi mana fatan alheri mun cimma matsayar barin jam’iyar NNPP, na shiga ADC don kawo sauyi da cigaba mai alfanu,”kalamansa.






