Jigo A Jam’iyar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC A Sokoto

Jigo A Jam’iyar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC A Sokoto

Jigo A Jam’iyar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC A Sokoto

Jam’iyar PDP a jihar Sokoto ta yi rashin daya daga cikin jigogin jam’iyar a jiha in da ya ba da sanarwar sauya shekar daga jam’iyar zuwa APC mai mulki a jiha da kasa kan gamsuwa da jagorancin da ta samu a satin da ya gabata.

Alhaji Sarki Bello wanda yake a unguwar Gobirawa a birnin jiha ya bayyana matakin da ya dauka na sauya jam’iya a wurin taron walimar da ya shiryawa Hajiya Farida Musa Jauro kan mukamin da ta samu a gwamnatin Nijeriya in da aka yi mata na Manaja kan shirin koyawa ‘yan kasa sana’a da za ta kula da yankin Arewa wanda aka yi a dakin taro na Mabera dake Sakkwato.

“Wannan abin da na yi tunani ne na kashin kaina domin tafiyar Hajiya Farida Jauro  muna yin ta ne dari bisa dari da yardar Allah,” a cewar Sarki Bello.

Wannan matakin da ya dauka ya hadu da tasgaro in da wasu makusantansa suka nuna bijirewarsu ga matakin da ya dauka jim kadan bayan kammala taron.

Daya daga cikin makusantansa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wannan tafiyar ta komawa APC ba da mu aka yi ta ba, ya koma ne shi kadai domin mu PDP ba ta yi mana laifin komaai ba, kuma ko sauya sheka za a yi ai bah aka ake yi ba, yakamata ya zauna da mu sannan mu san makomarmu in da za mu koma.

Ya ce Sarki Bello bai yi wa kansa adalci ba ta yaya zai koma APC a gaban mai baiwa gwamna shawara ba ta hannun gwamna da kansa ba.