BASAKKWACE'Z PALACE PROGRAM
A yau zan fara da lissafo kayan kwalliyar da za ki buƙata kafin asami kwalliya ta fuska mai kyau da tsari, ku biyo ni dan jin sunayensu da amfaninsu a cikin kwalliyar mata.
1) Jagira
2) Concealer
3) Eye shadow
4) Eye liner, gel liner
5) Mascara
6) Foundation
7) Highlighter
8) Contour
9) Setting powder
10) Finishing powder
11) Lipstick, jambaki or lip glows
12) Moisturizer, primer da kuma makeup setting spray
13) Blush
14) Brushes set
15) Eye lashes
16) Brow gel
17) Shimmer
18) Beauty blender sponge(BBS)
Ku biyo ni domin jin bayaninsu daya bayan daya:
1) Jagira wani nau'i ne na kayan kawalliya data ke zuwa a mazubi kamar haka :
*tanazuwa a yanayi na pencil da kaloli daban-daban ja, baƙa, brown dadai sauransu
*tanazuwa amatsayin gari da ake dangwalawa da brush wajen zana ta wato( gel liner)
Ana amfani da ita wajen zana gira ma' ana bin layin sama da ƙasa nagira da kuma cike shi, sannan ana iya sawa a saman ido amatsayin eye liner sannan ana sawa a kasan ido amatsayin kwalli.
2) Concealer: ana amfani da ita ne wajen gyara gira bayan zana ta da jagira kowani nau'i na jagirar dan daidaita giran yabada shape me kyau, kuma ana amfani da ita wajen ɓoye tabo ko ƙuraje na fuska, sannan ana gyara karkacewar eye liner da ita asaman ido da ita, ana gyaran baki da ita in ansa jam-baki ya karkace ko yahaura saman bakin ko ƙasansa, sannan ana highlighting da ita. Tana zuwa a nau'i kala kala
tana zuwa nau'i kamr pencil
tana zuwa a nau'i tube da kuma mazubi kamar na kwano ko faranti.
3) Eye shadow wani nau'in kayan kwalliya ne da ake amfani da shi wajan ƙawata kwalliya, ana sashi ne a saman ido wani lokacin ma harƙasan ido, kuma ana iya sashi a saman leɓe (tsakiya) bayan an shafa kalar jam-bakin da ake so. Yana zuwa a mazubi kala kala kamr haka:
le="font-size: large;"> yanayi na pencil,
yanayi plate da yake zuwa da kala.
4) Eye liner da gel liner: suma suna ƙawata kwalliya ne ta ƙara armashi, ana sa su ne a saman ido bayan an shafa eye shadow, ana kuma iya shafa su a saman ido ko ƙasan ido su kaɗai. Suna zuwa a yanayi kamr haka:
mazubi kamr na tube
tana zuwa a nau'in gari da ake iya kawaɓawa.
5) Ma
scara: ana amfani da ita ne wajen tazan gashin ido ya tashi ya yii kyau, yana zuwa a mazubi kamar na tube.