Jam'iyyar APC Reshen Zamfara Ta Gudanar Da Zaɓen Shugabannin Mazaɓu
Da yake jawabi tun da farko a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a gidan gwamnatin Gusau, Gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ya bukaci magoya bayan babbar jam’iyyarsu da su fito su jefa kuri'ar su ga dan takarar da suke bukata. Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Honorabul Nasiru Mu’azu Magarya ya ce a shirye suke su karbi duk wani dan siyasar da ke son shiga APC, domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a jihar. “Mun yi duk abin da ya dace don ganin mun kawo dukkan mambobin da suka koka kan wata matsala ko ganin ba muyi masu dai dai ba cikin wannan tafiya tamu domin ciyar da jam’iyyar gaba.
Jam'iyyar APC Reshen Zamfara Ta Gudanar Da Zaɓen Shugabannin Mazaɓu.
Daga Aminu Abdullahi Gusau
A yau(assabar) ne aka zabi jami’an da za su tafiyar da harkokin jam’iyyar APC a matakin mazabu a jihar Zamfara.
An gudanar da zabukan a duk fadin mazabu guda 147 dake a jihar ta Zamfara, kuma ya yi nasara, duba da yadda dimbin magoya bayan jam’iyyar APC suka fito domin gudanar da aikin daya dace su gudanar don kare ‘yancinsu na ‘yan kasa.
Wakilin mu wanda ya sa ido a kan yadda zaben ya gudana a kana nan hukumomin Gusau da Talata Mafara ya ce duk wadanda suka cancanci kada kuri’a, masu biyayya ga jam’iyyar sun fito kwansu da kwarkwata sun kada kuri’unsu ga dan takarar da suke so.
An gudanar da taron zabukan ne cikin yanayi mai kyau, domin babu wani rahoto na karya doka da oda, tun daga farko har zuwa karshe, kuma an zabi wasu daga cikin jami’an ne ta hanyar amincewa.
Da yake jawabi tun da farko a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a gidan gwamnatin Gusau, Gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ya bukaci magoya bayan babbar jam’iyyarsu da su fito su jefa kuri'ar su ga dan takarar da suke bukata.
Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Honorabul Nasiru Mu’azu Magarya ya ce a shirye suke su karbi duk wani dan siyasar da ke son shiga APC, domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a jihar.
“Mun yi duk abin da ya dace don ganin mun kawo dukkan mambobin da suka koka kan wata matsala ko ganin ba muyi masu dai dai ba cikin wannan tafiya tamu domin ciyar da jam’iyyar gaba.
Shi ma da yake magana a wajen taron, wanda jam’iyyar APC ta kasa ta turo domin kula da sabunta da rajistar jam’iyyar, da sake ingantawa da kuma tabbatar da anyi zaben a wannan jihar Alhaji Ibrahim Masari ya ce “Duk dan jam’iyyar da bai yi rajista a karkashin kwamitin sa ba, kuma bai halarci taron na yau a karkashin kulawar kwamitin sa ba, bai kamata ya dauki kansa a matsayin dan jam'iyyar APC a Zamfara ba.
“Za mu gudanar da taron na Ward Congress na gaskiya da adalci wanda kuma zai tabbatar da yadda za a yi nasarar gudanar da na kananan hukumomi da na jiha.” Masari ya kammala.
managarciya