Home Siyasa Jam’iyyar ADC ta soki Tinubu bisa halartar bikin kamun kifi na Argungu...

Jam’iyyar ADC ta soki Tinubu bisa halartar bikin kamun kifi na Argungu duk da ƙara yawaitar matsalar tsaro

8
0

Jam’iyyar adawa ta ADC ta soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa halartar wani bikin kamun kifi alhali matsalar tsaro na ci gaba da addabar wasu sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce Shugaban Ƙasa ya nuna halin ko in kula ta hanyar halartar bikin shekara-shekara na Argungu a lokacin da ake kashewa da kuma sace ’yan Najeriya da dama.

“Mun damu matuƙa cewa a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara, Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojoji yana Argungu yana halartar bikin kamun kifi, alhali rahotanni masu inganci sun nuna cewa kusan ’yan Najeriya 1,300 ne aka kashe cikin kwanaki 41 da suka gabata,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa: “Har yanzu dai, ’yan Najeriya marasa laifi da Iyalai suna ci gaba da ɗaukar mummunar illa da radadin ta’addanci, yayin da Shugaban Ƙasa ke shagulgula a wani biki.

Haka kuma ADC ta bayyana damuwa kan wani bidiyo da ake zargin ’yan ta’adda ne suka fitar, waɗanda ake alaƙanta su da sace-sacen mutane na baya-bayan nan a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here