Jami’in tsaron sa-kai a Sokoto ya kashe kansa bisa kuskure yayin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Jami’in tsaron sa-kai a Sokoto ya kashe kansa bisa kuskure yayin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Wani jami’in Kungiyar Tsaro ta Al’umma ta Jihar Sokoto (wanda aka boye sunansa) ya hallaka kansa bisa kuskure bayan aikin hadin gwiwa na ceton mutane 66 da aka yi garkuwa da su a jihar.

Aikin ceton ya gudana ne a ranar Litinin karkashin jagorancin sojoji a dajin Tidibali, gabashin jihar.

Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a yau Laraba, Mashawarci na Musamman ga Gwamna Ahmed Aliyu kan Sha’anin Tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya ce jami’in ya rasu sakamakon harbin bindiga bisa kuskure.

“Lamarin ya faru ne jim kadan bayan sun koma sansaninsu daga aikin ceton.

“Ya kasance tare da bindigarsa lokacin da ta harba a kuskure, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa,” in ji shi.

A cewar Usman, an samu nasarori da dama a ayyukan da ake gudanarwa don murkushe ‘yan ta’adda a jihar, wanda gwamnatin jihar ke daukar nauyi.