Jami'ar Usman Danfodiyo ta yi sabon shugaba

Jami'ar Usman Danfodiyo ta yi sabon shugaba


Jami'ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato ta nada Farfesa Bashir Garba matsayin sabon shugaban jami'ar.
Shugaban zartawar jami'ar Farfesa Attahiru Jega(Pro-chancellor)  ne ya sanar da hakan bayan cimma matsaya kan Farfesa daga cikin wadan da suka nuna sha'awar tsayawa don neman shugabancin sama da mutum 10.
A bayanin da ya fitar a jihar Sakkwato ya nuna yanzu jami'ar ta yi sabon shugaba, kafin nada Farfesa Bashir shi ne shugaban jami'a mallakar jihar Sakkwato.
Ya taba rike kujerar Sakataren gwamnatin jiha da zama shugaban makarantar fasaha da  kere-kere ta jiha.
Farfesa yana kwarewa a aikin gwamnati.