Home Uncategorized Jami’an Tsaron ‘Civil Defence’ Sun Fitar Da Sunayen Mutane 5000 Da Za’a...

Jami’an Tsaron ‘Civil Defence’ Sun Fitar Da Sunayen Mutane 5000 Da Za’a Ɗauka Aiki

3
0
Hukumar tsaro ta ‘Civil Defence’ ta fitar da sunayen mutum 5000 da su ka samu nasara a ɗaukar aikin da za ta yi a 2022.
Aisha Rufai, Sakatariyar Hukumomin  ‘Civil Defence’, Gidajen Gyaran Hali, da ta  Kula da Shige da Ficen Ƙasa ce ta baiyana haka a taron manema labarai a yau  Alhamis a  Abuja.
Ta ce hukumar ta kammala tsare-tsaren ɗaukar aikin na 2019, inda ta yi kira ga waɗanda su ka nemi aikin da su duba shafin ta na yanar gizo.
Ta ce waɗanda a ka tantance za su duba sunayen su a adreshin yanar gizo na http://cdfipb.carees da ga 17 ga watan Janairu domin samun ƙarin bayanai, inda ta ƙara da cewa sai waɗanda su ka samu nasara ne kawai za su iya buɗe shafin.
A cewar ta, shafin ba zai buɗewa waɗanda ba su samu nasara ba.
Ta ce a ranar 31 ga watan Janairu za a fara ɗaukar bayanai da karɓar takardun waɗanda a ka ɗauka aikin.
A nashi ɓangaren, Kwamanda-Janar na Hukumar, Ahmed Audi ya ce ɗaukar aikin tun na 2019 ne, in da ya ce bayan an gama tattara bayanai da takardun waɗanda a ka ɗauka aikin, sai kuma su shiga sansanin horo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here