Jami'an tsaro sun kuɓutar da mutane Shida a jihar Kebbi

Jami'an tsaro sun kuɓutar da mutane Shida a jihar Kebbi
Haɗin guiwar jami'an tsaro a jihar Kebbi sun samu nasarar kuɓutar da mutane shida da aka yi garkuwa da su da shanu da aka sace.
Mutanen da dabbobin an sace su ne a ƙauyukan Ukuhu da Kokanawa a karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar.
Daraktan tsaro a ma'aikatar jiha Abdurrahama Zagga ne ya sanarwa manema labarai nasarar da aka samu a ranar Talata ya ce samamen ya faru ne bayan umarni da aka samu daga gwamnan jiha Dakta Nasiru Idris bayan ya samu  bayanan sirri  yankin.
A cewar Zagga tawagar jami'an tsaro sun gano ɓarayin ta gefen wani gulbin Zamfara a in da suka kuɓutar da mutanen da dabbobin, sai dai 'yan bindigar sun tsere a lokacin da aka kai masu samamen.
"Mutane da aka karɓo an hannunta su ga iyalansu, wanan abin farin ciki ne ga gwamna musamman a cigaba da samu na  goyon bayan jami'an tsaro, hakan zai sa a samu ingantar tsaro a yankin masarautar Zuru"
Ya nuna fatar da suke da ita na kawar da ɓarayin shanu da 'yan bindigar Lukurawa a yankin Zuru da Argungu.