Home Rahoto Jami’an tsaro sun kashe ‘Yan bindiga 65 a Zamfara

Jami’an tsaro sun kashe ‘Yan bindiga 65 a Zamfara

4
0

Jami’an tsaro sun yi nasara kawar da ‘yan bindiga sama da 80 a jihar Zamfara ciki har da Kachalla Iliya Sarki sanannen dan bindiga da ke addabar yankin Tsafe a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Sarki ɗa ne ga ɗaya daga cikin jagororin ‘yan bindiga a yankin Arewa waton Ado Allero.

“Daga yammacin jiya Assabar zuwa yau Lahadi jami’an tsaron soja da ‘yan sanda da Civilian JTF na Borno sun yi arangama da ‘yan bingiga a garin Ƙuncin Kalgo, an samu nasarar da ba a taɓa samu ba duk wani babban ɗan bindiga da ke yankin nan an kashe shi kama daga babban ɗan Ado Allero Sarki, an kuma kashe Mai Rasha an samu nasarar kashe ɓarayin 80 zuwa 100.”

“Mutanen yankin suna cikin farinciki da jin daɗi domin ‘yan bindigar sun hana mutane zaman lafiya duk kasuwanci ya tsaya a yankin,” a cewar majiyar da ke garin Ƙuncin Kalgo.

Mai magana da yawun rundunar soja ta Fansan Yamma, Kaftin David Adewosi ya tabbatar da faruwar arangamar ya ce an yi ba ta kashi da ‘yan bindigar gefen Allero a ranar Asabar a Tsafe abin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga da dama.

Kaftin bai fadi adadin waɗanda suka mutu ba amma ya ce an kashe ‘yan bindiga masu yawa.

Shafin Facebook na hukumar sojoji ta ƙasa ta wallafa an kashe ‘yan bindigar 65 a musayar wutan da aka yi da ‘yan bindigar a Tsafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here