Jami'an Tsaro Sun Kashe Shahararren Dan Bindigaar Da Ya Addabi Mutanen Kaduna

Jami'an Tsaro Sun Kashe Shahararren Dan Bindigaar Da Ya Addabi Mutanen Kaduna

 

Shahararren Dan Bindigar Nan Wanda Ya Addabi Jihar Kaduna Dogo Maikasuwa Ya Gamu Da Ajalinsa

 
Daga Abbakar Aleeyu Anache 
 
Jami’an tsaron Najeriya sun bindige wani kasurgumin kwamandan ‘yan bindigar da suka addabi jihar Kaduna mai suna Dogo Maikasuwa.

 
Dan ta’addar na yawan sanya kakin sojoji, sannan yana rike bindiga kirar AK47 kuma a cikin kakin na sojoji ne aka kasha shi a cewar sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar.
Gwamnatin Kaduna ta fitar da sanarwar wannan nasarar tare da miyagun kayan da aka samu tare da shi.

Jami'an tsaro suna samun nasara kan 'yan bindigar a wannan lokacin abin da ake fatar hakan ya ci gaba su samu nasarar kakkabe su gaba daya.