Jami’an tsaro sun kama wani mutum da ake zargi da kai wa ’yan bindiga bayanai game da al’ummar Romo da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a Jihar Sokoto.
An bayyana wanda ake zargin da suna Ashiru Abubakar, ɗan ƙauyen Gumfa Gebe da ke ƙaramar hukumar Wamakko a jihar.
Rahotanni sun ce ana zargin Abubakar da yin aiki tare da wasu masu aikata laifuka a yankin Tambuwal.
Ana kuma tunanin wanda ake zargin na da hannu wajen isar da saƙon barazana ga mazauna Romo, inda aka ba su wa’adin biyan Naira miliyan 10 ko kuma su fuskanci hari.





