INEC ta yi waje rod da Lawan; ta tabbatar da Hon. Machina a Yobe

INEC ta yi waje rod da Lawan; ta tabbatar da Hon. Machina a Yobe

Daga Shamsudeen Yobe.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta yi waje rod da Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Lawan tare da tabbatar da Bashir Machina a matsayin halastaccen dan takarar Sanatan Arewacin Yobe, a zaben fidda-gwani da jam'iyyar APC ta gudanar, a cikin rahoton da ta fitar da yammacin yau (Jummu'a). 

A cikin sahihan bayanan turakarta (CTC) hukumar zaben ta shaidar da cewa ta tura tawagar jami'anta domin sanya ido a zaben fidda-gwani wanda Omale Samuel ya sanya wa hannu, ranar 28 ga watan May, 2022, wanda Hon. Machina ya samu quri'u 289 daga adadin quri'u 300 wadanda deligat su ka jefa a zaben. 

Har wala yau kuma, shima ofishin hukumar INEC daga jihar Yobe ya tabbatar da cewa an gudanar da wannan zaben fidda-gwani ne na Sanatan Arewacin Yobe (Zone ‘C’) tare da bayyana cewa ya gudana ne a Goverment Lodge da ke Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade a jihar.

Shiyyar Arewacin Yobe (Zone C) ta kunshi kananan hukumomin Bade, Yusufari, Jakusko, Nguru, Karasuwa, da Machina.

Haka zalika, rahoton ya shaidar da cewa zaben fidda-gwani ya fara ne da misalin karfe 11:30 na safe kamar yadda aka tsara gudanar dashi tare da samun halartar jami'an tsaro, jami'an hukumar zabe tare da na jam'iyya hadi da masu jefa kuri'a daga wadannan kananan hukumomin a inda zaben ya wakana.

“A hannu guda kuma, jim kadan kafin fara zaben, dukan yan takara tare da shugabanin jam'iyyar sun hallara tare da dalaget a wannan muhallin da aka gudanar da zaben."

“Haka kuma, zaben fidda-gwani ya gudana a karkashin kulawar babban jami'in hukumar INEC, Alhaji Danjuma Isa Munga."

“Sannan kuma, an fara zaben bayan an bude taron da addu'a ta bakin Sakataren Kwamitin tsare-tsare, Alhaji Lawan Modu Sheriff.” In ji rahoton. 

Zaben fidda-gwani jam'iyyar APC na Sanatan Arewacin Yobe ya jawo cece-kuce biyo bayan ayyana Hon. Bashir Machina, tare da tsayin daka cewa ba zai janye wa Shugaban majalisar dattawan Nijeriya ba, Ahmad Lawan, bayan da ya sha kaye a zaben fidda-gwani na shugaban kasa.

Sanata Lawan ya sayi tikitin takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC tare da maigidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. 

Duk yadda Lawan bai shiga zaben fidda-gwani Sanatan Arewacin Yobe ba, amma kuma uwar jam'iyyar APC ta kasa ta mika sunan sa ga hukumar zaben INEC a matsayin shi ne dan takarar da ta ke son ya yi takarar Sanatan Arewacin Yobe a zaben 2023, al'amarin da ya tayar da kura a kafafen sada zumunta.