Inec a shirye take ta jagoranci zaɓuka a ƙananan hukumomi idan aka ba ta dama

Inec a shirye take ta jagoranci zaɓuka a ƙananan hukumomi idan aka ba ta dama

Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya ya ce a shirye suke su gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar idan aka ba ta damar yin hakan, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kalaman na Farfesa Mahmood Yakubu na zuwa ne 'yan makonni bayan Kotun Ƙolin Najeriya ta bai wa ƙananan hukumomin 'yancin cin gashin kansu a harkokin kuɗi, tare da umartar gwamnatin tarayya kada ta bai wa kowace ƙaramar hukuma kasonta matuƙar babu zaɓaɓɓen shugaba.

Daga nan ne kuma wasu 'yanmajalisar tarayya suka fara yunƙurin goyon bayan dokar da za ta ƙwace alhakin gudanar da zaɓen hukumomin daga hannun gwamnatocin jiha zuwa hukumar zaɓe ta ƙasa Inec.

Sai dai da yake magana lokacin da ya bayyana a gaban kwamatin majalisa kan harkokin zaɓe, Farfesa Yakubu ya koka kan kuɗaɗen gudanar da zaɓuka a ƙasar.

A shekarar nan Inec za ta gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Ondo da Edo da ke kudancin ƙasar, kuma abin da ya kai shi majalisar kenan a yau Alhamis