Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya nesanta kansa da jaddada goyon baya ga shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu.
Sanatan, wanda ya shafe sama da shekaru 20 a majalisar dokokin kasar, ya kasance bako a shirin Siyasa na ran Lahadi a gidan Talabijin na Channels.
A cewarsa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu amincewar gwamnonin jam’iyyarsa ta PDP 22 a zaben 2015 duk da haka ya sha kaye a zaben a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
Channels TV ta tuna cewa a ranar 22 ga Mayu, 2025, gwamnonin jam’iyyar APC 22 ne suka amince da Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa.
Ndume, jigo a jam’iyyar APC, ya ce bai goyi bayan matakin da gwamnonin APC suka dauka ba, saboda “abubuwa sun yi muni matuka a kasar nan” a halin yanzu.
Ya koka da irin mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da tsadar rayuwa a kasar da kuma matsalar rashin tsaro da ke addabar sassan Najeriya,” in ji shi





