Ina tausayin Tinubu domin gwamnonin PDP 22 ne su ka marawa Jonathan baya amma ya fadi zaɓe a 2015 - Ndume

Ina tausayin Tinubu domin gwamnonin PDP 22 ne su ka marawa Jonathan baya amma ya fadi zaɓe a 2015 - Ndume

Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya nesanta kansa da jaddada goyon baya ga shugaba Bola Tinubu na neman wa'adi na biyu.

Sanatan, wanda ya shafe sama da shekaru 20 a majalisar dokokin kasar, ya kasance bako a shirin Siyasa na ran Lahadi a gidan Talabijin na Channels.

A cewarsa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu amincewar gwamnonin jam’iyyarsa ta PDP 22 a zaben 2015 duk da haka ya sha kaye a zaben a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

Channels TV ta tuna cewa a ranar 22 ga Mayu, 2025, gwamnonin jam’iyyar APC 22 ne suka amince da Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa.

Ndume, jigo a jam’iyyar APC, ya ce bai goyi bayan matakin da gwamnonin APC suka dauka ba, saboda “abubuwa sun yi muni matuka a kasar nan” a halin yanzu.

Ya koka da irin mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da tsadar rayuwa a kasar da kuma matsalar rashin tsaro da ke addabar sassan Najeriya," in ji shi