INA SO...: Labarin Soyayya Mai Al'ajabi Da Burgewa, Fita Ta Biyu

INA SO...: Labarin Soyayya Mai Al'ajabi Da Burgewa, Fita Ta Biyu

INA SO...



*LITTATTAFAINA*

*FATIMA ZAHRA SA'EED*
*RANA DAYA TAK!!!*
*JARIRAI*
*SIDDABARU*


Da sunan Allah mai Rahama
mai jin kai.
Allah ka yi salati ga shugaban halitta Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wa'sallim.


*GODIYA*
Ta tabbata ga Allah buwayi da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi mai suna INA SO... Ina rokon Sa ya sa in fara lafiya in gama lafiya amin.

*YABAWA*
Ga yayata daya kwal a duk cikin tarin marubuta, wato Nana Aisha Hamisu Abdullahi, Allah ya dafa miki amin.


*Page 3/4*

*RANAR FARKO.*

Yana fakawa da gabjejiyar motarshi a gurin parking tana sauka daga adaidaita sahu. Da yake ta san yau ba ta makara ba don haka komai a nutse take yi babu gaggawa irin ta jiya.

Ta tsallaka titi a hankali ta nufi cikin Mall ɗin, suka gaisa da masu gadi kamar yadda ta saba sannan ta wuce ciki.

Ya fito daga cikin motar tashi, daga ɗaya ɓarin ma Sadiq ya fito. Nan da nan masu gadi da sauran ma'aikatan dake waje suka ƙarasa da sauri suka miƙa gaisuwa.

A gadarance yake amsa musu cikin izza sannan ya sa kai ya nufi cikin Mall ɗin yana karkaɗa 'ya'yan mukulli, Sadiq na biye da shi. Yana shiga ma'aikata suka fara miƙewa tsaye suna miƙa  gaisuwa ciki har da Halima, a daidai saitin gurinta ya tsaya ya yi ƙasa da murya ya ce. “Ki same ni a ofice!”

Da sauri a rikice ta ɗaga kai ta dube shi. Ta kwaso wata uwar in'ina. “Ran... ranka... ranka ya daɗe ina... Ina ne ofis ɗin?”

“Ki hau sama ki tambayi Manaja da kanshi zai kawo ki har ofis ina.” Cikin matukar ɗaure fuska ya faɗa, daga bisani ya juya ya dubi Sadiq.

“Let’s go!”

Ta sauke wani gwaggwaɓan numfashi tana ji babu daɗi a ranta, alamu sun nuna dai wannan mutumin zai zame mata ƙalubale a wannan gurin aikin nata.
Komawa ta yi ta zauna tana hangen Ladidi na ƙunshe dariya a baki ea hannayenta biyu, ta kawar da kai zuwa ga wata customer da ta kammala sayayya ta zo wajen biyan kudi, sai da ta sallame ta sannan ta dubi Najib maƙocinta ta roƙi alfarmar ya cigaba da aikin kafin ta dawo, dama duk aiki ɗaya suke yi.


A ofishin Manaja bayan ta gaishe da shi cike da girmamawa ta tambaye shi ofis ɗin Ali.

Da sauri ya ɗaga kai ya kalle ta cikin buɗe idanu. “Hala ba ki san wane ne shi da matsayinsa a nan ba ko?”

Ta rausayar da kai. “An faɗa min cewa yaron Alhaji ne ko?”

“Shi ne kuma kike faɗar sunanshi haka babu girmamawa, ko ba ki ga kowa yana ba shi girma ba ciki har da ni?”

Ta yi ƙasa da kai cikin jin yanayi mara daɗi a ranta.
 
Malam Jafar Manaja ya ƙara da cewa. “Kodayake ba ki jima sosai a nan ba shiyasa ba za ki san matsayinsa da irin makauniyar soyayyar da mahaifinsa yake yi masa ba, amma ba komai ai na san kin fahimci hatta guraren nan da sunanshi ake amfani ko?”

“Zan kiyaye gaba in sha Allah.” Ta faɗa murya cike da rauni.


Da kanshi ya jagorance ta har zuwa wani ɓangare daban wanda tun da ta fara aiki ba taɓa shiga ba.

A iyaka abin da idanunta suka gane mata ba karamin tsaruwa sashen ya yi ba, ta san ofis ɗin kuwa sai abin da ido ya gani.

Ƙwanƙwasa ƙofar ta fara yi, daga ciki ya ba da umarnin ta buɗe ta shiga. Da sallama ta shiga ofis ɗin cikin ɗari-ɗari. Wani sanyi mai mugun daɗi a jiki ta ji ya fara ratsa ta a hankali, yayin da kuma ƙamshin turaren ɗaki da ya gama gauraye ko ina ya fara shiga ƙofofin hancinta da sannu-sannu.

Ta dirice ta rasa abin da ya kamata ta yi a lokacin. Shi kuma gogan ya yi shiru ya kawar da kai yana sabgoginsa a waya tamkar ba shi ya kira ta ba. Sadiq ma hankalinsa na kan waya sai dai ya ɗaga kai lokaci-lokaci ya kalle sannan ya mayar ya cigaba da harkokinsa.

“Ranka ya ɗade ga ni.” Ta faɗa a gajiye da muryarta a can ƙasan maƙoshi.

Wani wulaƙantaccen kallo ya watso mata kana daga bisani ya cuna mata gefen da kujeru suke a ajiye da leɓen bakinsa ya ce. “Zauna ina zuwa.”

Tuni ta zauna tana ajiye numfashi, damuwa mai yawa ta fara ziyartar zuciyarta. Ta tabbata dai wannan bawan Allah so yake ya wulaƙanta ta hakan nan ba tare da ko kallon banza ta taɓa yi masa ba.

Sai da ya kwashe kusan mintuna goma tana nan a zaune ita bai ce mata ta tafi ba kuma bai ce mata komai ba, yana can yana shafe-shafen waya.
Ajiye wayar ya yi ya ɗaga kansa ya dube ta bayan ya kwashe ƙafafunsa ya zuba su a saman faffaɗan teburin dake girke a gabanshi ya ce.

“Meye ma sunanki?”

“Halimtu Sadiya.” Ta amsa.

Ya girgiɗa kai. “Kin san me nake so da ke?”

Ta jijjiga kai alamar a'a.

“Wannan abin na fuskarki nake so ki cire... Ina so in ga larurar da aka ce kina da ita da ta saka kike ɓoyon fuska.”

Jikinta ya soma rawa, ta fara jin tsoron kar wannan mutumin ya keta mata haddinta, tana tsoron kar ya yi amfani da ƙarfin ikonsa ya tilasta mata buɗe fuskarta ba tare da ta shirya.

Girgiza kai ta soma yi, muryarta cike da rauni ta ce. “Ka yi hakuri, ba zan iya buɗe fuskata ba, akwai babbar matsala yin hakan.”

Ranshi ya fara ɓaci, fuskarshi ta nuna haka.
“Wai uban meye a fuskar taki da ba za ki buɗe ba?”

Ta soma kuka duk da babu wanda yake ganin idanunta.

“Ka yi wa girman Allah ka rufa rayuwata asiri kar ka matsa min a kan sai na buɗe fuskata...”

“Idan kin ga kin fita daga gurin nan to ki tabbatar kin buɗe min fuskarki na gani... Amma kafin sannan bari in faɗa miki wani abu da baki sani ba...”

Ya ajiye ƙafafunsa a ƙasa ya miƙe ya fara taku ya nufo ta, sai da ya zo daidai saitin ta ya tsaya ya rankwafo kanta yadda har tana iya jin hucin numfashinshi ya ce. “Rashin narasa ba ta daga cikin ƙaddarata, ban taɓa sanyawa a raina ina son wani abu na rasa ba... Saboda haka ina so ki tabbatar wa da kanki tun da na ji INA SO in ga fuskarki to babu makawa sai na gani, a yanzu a take!”

Ta tsorata sosai da yanayinsa, hakan ne ya saka ta zabura ta miƙe da sauri tana ja da baya.

Ta fara yi masa magiya da roƙo a kan ya ƙyale ta saboda son da yake yi wa iyayenshi amma tamkar busar sarewa take yi masa a kunne, idanunshi sun rufe ya fara ƙoƙarin saka ƙarfi ya fizge niƙabin fuskar tata.

Ba ta san lokacin da ta saka hannaye bibiyu ta riƙe masa nasa hannuwan ba da duk ƙarfinta. Abin da ba ta taɓa yi ba a rayuwarta yau ya sa ta yi, wato ta riƙe hannun wani namiji wanda ba muharraminta ba. Kuka take yi sosai tana cigaba da roƙon shi da roƙon Sadiq a kan ya saka baki ya ƙyale ta, amma Sadiq ya yi fumfurus ya ƙi yin ko ƙwaƙƙwaran motsi.

Saura ƙiris ya yi nasarar fizge mata niƙab ɗin saboda yadda ƙarfinshi ya nunnunka nata, hannayenshi na riƙe gam cikin nata tana kuka tana girgiza masa kai tana faɗin “A’a! A’a!! A’a!!! Ba na so! Ba na so!!! A’aaaaa”. 

Ji suka yi an fara ƙwanƙwasa ƙofar ofis ɗin daga waje. Hakan ne ya tilasta masa sauke hannayenshi cikin matukar ɓacin rai.
Idanunshi kawai ya kai ga ƙofar bai iya bayar da umarnin a buɗe a shigo ba, can kuma sai ya ga an murɗa ƙofar an shigo. Alhaji Hadi Karma ne ya shigo, wato mahaifinshi.

Da ƙarfi Halima ta yi ajiyar zuciya tare da godewa Allah da ya kawo mata mafita a lokacin da ƙarfinta ya riga ya gama ƙarewa.

Fuskar Alhaji cike da murmushi ya dubi Ali.

“Kana tare da Malama Halima kenan? Tana cikin sabbin ma'aikatan da muka ɗauka ai.”

“To amma Daddy me ya sa aka ɗauke ta aiki bayan an ce ba ta taɓa buɗe fuskarta an gani ba? Ba a tunanin hakan zai zama matsala ga security gare mu.”

“Babu wata matsala my son, laurara ce ta sanya faruwa hakan, kuma bincike ya tabbatar da babu wata matsala.”


Wannan dama da Halima ta samu da ita ta yi amfani ta sulale ta bar ofis ɗin ta koma gurin aikinta zuciyarta a jagule.
 
Aikin wunin ranar gaba ɗaya ta yi shi ne cikin wani irin yanayi mara daɗi, taimakon da Allah ya yi mata ma shi ne har lokacin tashin ta daga aiki ya yi ba ta ara jefa Ali a idanunta ba saboda zuwan mahaifin nashi sun yiyyi wasu ayyuka ne da lissafe-lissafe a kan cigaban gurin. 

Koda ta koma gida ta so ta ƙara labartawa Umma abin da ya faru yau sai kuma ta ji tsoron sakamakon abin da hakan zai haifar, musamman in ta tuna yadda Umma ta shiga damuwa a jiya balle kuma abin da ya faru a yau ya ninninka na jiya.

Ta sani sarai ba ƙaramin aikin Umma ba ne ta ce kar ta ƙara zuwa gurin aikin muddin haka za ta cigaba da faruwa. Ita kuma tana tsoron rasa wannan babbar dama da ta samu da za ta tallafawa mahaifiyar tata da ƙannenta biyu don su huta da wahalar duniya.

Hakan ne ya sa ta yi ƙaryar cewa kanta na ciwo, don haka tana cin abinci ta nemi guri ta kwanta dayake ita din ba ma'abociyar ƙaunar shan magani ba ce, babu yadda Umma ba ta yi ba a kan ta sha paracetamol ɗin da ta aika Auta ta sayo, amma ƙememe ta ƙi sha ta ce in ta samu bacci ma shikenan ciwon kan zai tafi.


*******

A nashi ɓangaren kuma tun fitar Halima daga ofis ɗin nashi bai wani mayar da hankali a kan abin da ya kawo Daddyn nashi su yi ba. Gaba ɗaya hankalinshi na ga Halima da tunanin yau ta yi nasara a kanshi, karon farko kenan da aka taɓa cin nasara a kanshi.

In ya tuna hakan ba ƙaramin ƙuna ranshi yake yi mishi ba, abin da yake ƙara ba shi haushi shi ne yadda tunda suka taho a hanya Sadiq ke yi masa dariya da shegantaka a kan diramar tasu da kuma yadda yau aka ci shi da yaƙi.

Bai biyewa Sadiq ba don kar zafin zuciya ya sa ya kai masa mummunan naushi, ba ƙaramin aikinsa ba ne hakan. Ya san cewa akwai gobe, in yau ta kuɓuce masa ai gobe na nan, dama kuma kwana uku ya ba wa kanshi, don haka gobe ya shirya ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai ya buɗe mata fuskar ya gani, ba ma zai tsaya yi mata wata magana ba kawai hannu zai saka ya cire niƙab ɗin kai tsaye ya cillar gefe.

In ya tarar da cewa ita ɗin mummuna ce da take sakaye munin nata a cikin niƙab da tabarau ya ci alwashin tozarta ta a gaban sauran ma'aikata, in kuma irin bilichin ɗin nan ta yi ya babbake mata fuska nan ma za ta sha ƙasƙanci. Kai duk wani tazgaro da ya tarar a fuskar tata to tabbas sai ya muzanta ta da kyau yadda ba za ta ƙara marmarin yin jayayya da shi ba a gaba! Wannan shi ne tunaninsa.

Gidansu Sadiq ya fara biyawa ya sauke shi, daga nan ya wuce zuwa wani jangul da 'yan shaye-shaye suke cin dabdalarsu.

Daga nesa kaɗan ya faka motar tashi ya ɗan sauke gilashin motar.

Goga wanda shi ne ja-gaba a jangul ɗin ya tashi da sauri ya nufi motar. Da ya isa sai da ya tsaya ya yi masa kirari irin na neman fada. Duk da ɓacin ran da yake ciki haka ya saki fuska kaɗan ya nuna godiyar shi ga goga sannan ya buaci a kawo masa BABBAR HAJA (Littafi na gaba).

“Ka daɗe ka yi karko na wajen Alaji!” Goga ya faɗa yana ƙara sara masa sannnan da sassarfa ya tafi zuwa inda suke ɓoye kayan aikin nasu ƙarƙashin wani rusheshen dutse, ya ture dutsen ya zaro ƙunshin wata baƙar leda, ya warware ta ya fara fita da sinƙi-sinƙin ƙulli na tabar wiwi. Ƙulli biyar wanda lissafinsu ya kama Naira dubu biyar ya tattara su ya naɗe a wata takarda sannan ya koma da sauri gurin Ali.

Naira dubu goma Ali ya duntso ya miƙa wa Goga sannan ya kunna motarshi ya wuce. Sai da ya tsaya a hanya ya kwashi kayan fruits sannan ya wuce gida.

Lokacin da ya isa magriba ta yi, maimakon ya wuce kai tsaye ya yo alwala ya yi sallah a'a, ai watsa ruwa kawai ya yi ya fito ya fara murza dular tabar wiwi ɗinsa.
Da ya gama tsaf sai ya cinna mata wuta ya fara zuƙar hayaƙi yana ambular da shi waje ta ƙofofin hanci cike da gwanancewa.

Nan da nan farin hallitar gilashin idonshi suka fara sauya launi zuwa ja-ja-ja baƙi-baƙi.
 
Ya cigaba da busar tabarshi yana cigaba da saƙa zaren tunanin yadda zai yi da Halima a gobe, tasirin hayaƙin taba da kuma ƙarfin sharrin zuciya suka cigaba da ingiza shi wajen ƙara jin haushin ta da cin mummunan alwashi a kanshi.

Jin ana ƙwanƙwasa masa ƙofa daga waje ne ya sa shi zabura da sauri ya murje guntun dular tabar wiwi ɗin a cikin wani ɗan karamin tray, ya ɗauki tray din ya tura ƙasan makeken gadonshi sannan ya yi hanzarin ɗauko room freshener ya fara feshe ɗakin.

Sai da ya tabbatar ƙamshin freshener ya gauraye ɗakin sannan ya nufi ƙofar ya buɗe.

“Mom!” Ya faɗa ƙasa-ƙasa.

Tsayawa ta yi tana ƙare masa kallo kafin ta saka kai zuwa cikin ɗakin tana cewa da shi.

“Na ga shigowar ka fa, amma sai na ji ka shiru ba ka fito ba...” Maganar tata ta maƙale sakamakon ƙamshin freshener da kuma warin wiwi da suka haɗu suka bayar da wani irin yanayi na daban a hancinta. Ta dinga buɗe ƙofofin hancinta tana shaƙar abin tana fesarwa kafin ta kyaɓe fuska ta dube shi.

“Mene ne wannan ka saka a ɗakin nan?”

“Freshener ce Mom!”

Ta yi saurin kallon shi. “Wace irin freshener ce haka mara daɗin ƙamshi? Anya ba wannan matsiyaciyar tabar taka ka sha ba shi ne za ka yi basaja da room freshener? Ni dai na san ba haka ƙamshin freshener ɗin nan yake ba.” Cikin tsattsare shi da idanu ta yi furucin.

Ya soma sosa ƙeya. “No Mom, ban sha komai ba.”

“Ƙarya kake wallahi, ga idanunka nan sun nuna.”

Ya shiru cikin ɓacin rai.

Ta ɓata fuska ita ma. “Son ba na so ka je jefa rayuwarka cikin matsala ta hanyar wannan zuƙe-zuƙen, Ka sani sarai yadda shan tabar nan yake da babbar illa ga rayuwa musamman ma matashi, me ya sa ba za ka raba kanka da sha ba?”

“Addu’a za ki cigaba da yi min Allah ya sa na daina.”
 
“Addu’a kullum ina yi maka Allah ya shirya ka.”

Ya amsa. “Amin.”

Ta ce. “Ka shirya ka fito mu yi dinner!”

Gyaɗa kai kawai ya yi, ta juya ta fice. Tana fita ya zaro tray ɗin nan ya sake murza wata dular tabar ya banka mata wuta don sam bai ji kanshi ya yi masa yadda yake so ba, ga shi ita ma Momsy ta zo za ta ƙara masa pressure don haka sai ya babbaka kanshi sosai da hayaƙi sannan zai fita ya je gurin nasu.

Wannan kenan!


*RANAR TA BIYU.*

Kamar dai Halima baki ta yi wa kanta don kuwa da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi tare da zazzafan zazzaɓi. Tana kwance rufe da bargo amma haƙwaranta sai karo suke da juna yayin da gangar jikinta ke ta rawa.

Hankalin Umma ya tashi sosai duk ta rikice.

“Tun jiya na matsa miki ki sha magani kika ƙi, da kin daure kin sha watakila da ciwon bai tsananta miki kamar haka ba.”

“Ina wayata Umma?” Ta faɗa da ƙyar.

“Me za ki yi da wayar kuma?”

“Manaja zan kira in bayar da uzurin rashin zuwa gurin aiki yau.”

Da sauri Umma ta dubi Maryam ta ce ta ɗauko wayar yayar tasu. Maryam ta kawo wayar. Cikin sassarfar harshe Halima ta ce wa Maryam ɗin ta lalubo lambar da aka rubuta Baba Manaja ta kira. Bayan kiran ya shiga an ɗaga ta hau katifar da yayar tasu take kwance ta kara mata wayar a kunne.

Da ƙyar Halima ke magana ta gaishe da Manaja sannan ta ƙara da cewa. “Na tashi da zazzafan zazzabɗɓi da ciwon kai mai tsanani, ina roƙon a yi min uzuri, wallahi ko tashi ba ina iya yi.”

Cike da alhini da tausayawa ya amsa. “Ayya! Subahallahi Allah ya sauƙaƙa miki ya ba ki lafiya, babu matsala duk lokacin da kika samu sauƙi kya dawo bakin aiki.”

“Yawwa na gode Baba.”

Ya katse kiran, ta ce ta lalubo lambar Ladidi ma, ita ma ta sanar mata da zazzaɓin da ta tashi da shi don haka yau ba za ta samu fitowa aiki ba. Daga nan aka kashe wayar aka ajiye.

Umma ta yi iyakar bakin ƙoƙarinta a kan Halima ta tashi ta sha magani amma ta ƙi, ta kuma ƙi cin komai hatta da ruwan koko da Umma ta dama musamman saboda ita ta samu ta saka abu mai ruwa-ruwa a cikinta amma ɗememe Halima ta yi wa bakinta mukulli ta ƙi.

Umma ta dubi Maryam. “Maryama ko Atine mai kyamis za ki je ki kira ta zo ta yi mata allura?”

Wata irin zabura Halima ta yi cike da shagwaɓa ta ce. “Allura kuma Umma?”

Umma ta ɗaure fuska. “E mana, tun da kin ƙi shan magani kuma kin ƙi ci da shan komai ai sai a zo a yi miki allura mana.”

“Umma kin san fa ba na son allura.”

“Hakan nan za ki daure.”

Ta juya ga Maryam. “Ke yi maza ki je ki faɗa mata kafin ta fita.”

Maryam ta amsa da to ta fice.


*Share please**
08164243585