INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta 12
Page 12
Lantai sai ajiyar zuciya take, ta kasa ko magana saboda uban kukan data ci.
Barbushe kuwa zuciyarsa kamar ta tsaga kurjinsa ta fito haka yake jinta, kukan yarinyar na ƙara fusata shi, yana saka shi cikin mugun yanayi na fusatar gaske.
Kallonta yake da jajayen idanunsa yana son tambayarta wanda ya taɓa ta amma don bala'in dake cin ransa ya kasa magana.
Kawai janyo wuƙa yayi ya dinga yankar jikinsa, wuƙar maimakon ta kama sai ta narke kawai duk ta lanƙwashe.
Kowa gun ya razana kada Innar shi ta ji labari ma duk tafi firgicewa tana addu'ar Allah Ya yayyafawa fitinar ruwan sanyi kawai.
Daga ƙarshe daya kasa magana kawai hannunta ya kama ya nufi waje nan da nan yaransa suka bishi ɗuu suna ihu tare da busa sarewar duk randa ƴan ƙauyen suka ji ta kowa ɓoyewa yake don sun san ran mazan ɓace yake duk wanda yayi karo da shi sai ya lahantashi .
Duk inda suka wuce tamkar anyi shara a garin don gudun bala'in Barbushe kowa ke yi a ƙauyen babba da yaro shakkar haɗuwa da Barbushe yake a ƙauyen indai suka ji wannan busar .
Lantai kuwa sai murna take a ranta ta kalli Barbushe ta ce da muryar kuka.
"Ba wai wata mata bace mai saida ƙosai dan naje siyen ƙosai gidanta tai ta zagina tana cemin wai na addabi kowa ƙauyen yanzu saboda lalacewa har wajen ɗan daba kamarka nake zuwa , sai na ji haushi na kifar da ƙullun ƙosan da man suyar shi ne ta kaini ƙara gun Mai gari ashe jawararsa ce ya sa akai min bulala da yawa shima ya amsa yayi min shi ne yau yace wai mu bar ƙauyen ya koremu bayan ya zazzage mu ni da Inna Kande."
"Waiyihuhu ! Ina ɗan banza ga ubanshi.
Ina ja'iri ga ubanshi .
Ina wake ja da ni ya kwana kiyama.
Fusatacce nake mai ɗauke jarumtar namiji .
Kowa yace jirani raggo ne cikar mazantaka a gwabza ko ba shiri.
Sai ni Barbushe uban kowane ƙolo jarumi nake uban sadaukai gaba da ni daidai yake da gaba da ajali.
Sai yaran suka ɗauka.
"Cau-cau maigida namiji kake uban mazaje kowa ce ba kai ba ya kwana kiyama.
Da ranka ya ɓaci gara ruwa ya cinye gari.
Da ka fusata gara an rasa rai .
Zaman kowa lafiya kana cikin walwala .
Yayan Nuratu ikon Allah maza basu sarewa sai dai su faɗi in sun faɗi kowa yasan sun fi uban wasu suna."
Tafe suke suna kirari suna ihu suna karta wuƙaƙe tartsatsin wuta na tashi sama .
Suna shigowa ƙauyen kowa ya fara ta kansa domin dai ba su manta yadda kwanaki Barbushe ya zo har nan cikin ƙauyen ba ya yi faɗa da ƙaurayen ƙauyen dukansu babu wanda bai lahanta ba.
Kai tsaye gidan mai gari suka nufa ba wata-wata Barbushe yace a kamo masa mai garin .
Yaran suka afka cikin gidan har ɗakin mai garin suka kamo shi suka fito da shi waje yanata alwalai ƙuda don tashin hankali.
Lantai na ganin yadda aka cafkoshi sai abin ya bata dariya ta kwashe da dariya .
Barbushe ya dubi Lantai cike da kulawa yace, "Ƙanwata shi ne wanda ya zaneki har ya koreki daga wannan ƙauyen ?
Lantai ta ɓata fuska ta ce, "Shi ne amma ba shi kaɗai bane akwai sauran su Liman."
Mai gari ya ji daɗin abin da Lantai tayi domin abin kunya ne ace shi kaɗai za a zane a gaban jama'arsa.
Nan da nan aka ce mai gari ya je ya tattaro jama'ar garin baki ɗaya su zo ƙofar gidansa hada Hure mai ƙosai.
Jiki na rawa mai gari ya nufi gidajen dattijan ƙauyen da kowa busar Barbushe tasa ya shige gidansa ya ɓoye.
Haka mai gari ya dinga bi gidajensu yana tattaro su, kowa ido ya raina fata kada bafaden daya fara dukan Lantai ya ji labari yafi kowa ruɗewa da shiga tashin hankali shi da mai gari sun san yau sai Allah zai ƙwace su hannun Barbushe.
Liman ya dubi mai gari rai ɓace yace, "Amma ranka ya daɗe baka kyauta min ba, kasan yarinyar ashe ƙanwar marar imanin nan ce amma ka zaneta kana cewa ka koreta ? To wai mu miye ruwanmu daka tattaro mu ne ?
Kowa sai ya taso ma mai gari da masifa akan me zai kirashi bayan shi ne ya tattago masifar da kanshi kamar ba mai garin da kowa ke masifar tsoro bane ba a gabansu.
Mai gari dai yau babu baki sai kunne, Allah kaɗai yasan yawan addu'ar da yake tare da kwashema Lantai albarka a zuciyarsa.
Haka su ka je gidan Hure mai ƙosai ta kuwa yi tsalle ta dire ta ce ita kam babu inda zata je wallahi ai ba cewa tayi ya daki Lantai ba balle ya koresu daga ƙauyen ba.
Mai gari ya fusata ya kife Lantai da mari yana cewa, "Don uwarki duk ba ke kika jawo mana masifar da tashin hankalin ba ? Sau nawa Lantai na kifar min da garin tuwon gidana ubanwa ya taɓa ji na gaya masa balle na kai ƙara ? Sau nawa tana zane mani yara ban cewa komi duk saboda gudun masifar da zata faru ? Lantai kowa yasan bata haƙuri da abin da akai mata daman me yasa ke baki yi haƙurin ba ?
Hure sai ta sake tsurewa ai, ta kama kuka tana ta shiga uku ta lalace ina zata saka kanta wallahi marainiya ce ita ba ɗa ba jika su taimaka su ƙyaleta ita ta amince zata gudu daga ƙauyen yanzu ta sauya wajen zama .
Ganin tana niyyar ɓata masu lokaci mai gari ya ja ta ƙiii sai ƙofar gidansa.
Zuwa lokacin duk wani magidanci yana ƙofar gidan mai gari da matashin saurayi anyi tsit ana jiran abin da zai biyo baya.
Musa kuwa sai sunne kai yake bai son Lantai ta ganshi ta ja masa bala'in daya fi na su mai gari domin yanzu yake jin haushin yadda ya saki baki yake gaya mata Barbushe mugu ne.
Sai duƙewa yake yana jan duk addu'ar data zo bakinsa.
Inna Kande kuwa zuwa yanzu ta tabbatar da Lantai ta zama abin da ta zama a ƙauyen don haka sai kawai ta koma gefe guda ta zubawa sarautar Allah ido , tasan dai a duk cikin iyayen Lantai babu mai irin fitina da rigimar Lantai ko ina ta yo gadon wannan halin ?
Barbushe ya dubi mai gari ya tangare masa ƙeya yace, "Tsoho wane ɗan jakar ubanne ya baka wannan ƙauyen da har kake iƙirarin korar ƙanwata Nuratu daga cikinsa ?
Mai gari yayi wuƙi-wuƙi yana alwalai ƙuda don bai da ta cewa ɓarawo hannun mata.
Wani yaron Barbushe ya ɗaga adda yana nuna cikin mai gari yace, "Sai na zubo da ƴan hanjinka fili zakai bayani tsoho ?
Mai gari ya kwanta ƙasa ya kama ahi yana ayi masa afuwa sharrin tsufa ne yasa shi aikata hakan.
Lantai ta dube shi ta ce, "Dukan nawa fa shima sharrin tsufan ne ?
Mai gari kamar ya saki zawo don firgita yace, "Wane irin duka kuma ba daɗin faɗi Lantai? Ai ke kika zane ni sarai wallahi ni kam ban zane ki ba ."
Lantai ta kamo hannun Barbushe ta saka kuka "Yayana ka tambayi mutanen wajen nan gabansu ya kamani ya zane sarai harma suna ƙara zuga shi wai ya kyauta ban daku ba, kowa da abin da yake cewa ."
Barbushe ya watsa masu kallo sai ga dattijai an soke kai ƙasa ana addu'ar samun tsira daga sharrin Lantai.
"Yauwa gama Musa can ai sai da mu kai labarin da shi dana koma gida ko Musa ? Ta kalli inda Musa yake ta jefa masa tambayar.
Musa kuwa yasan hada Babansa a wajen taya zai amsa a zane Babansa a gabansa ?
Ta lalle shi ta ce, "Ko da yake kace kai daman baka shiga harka indai akwai Yayana wai shi ɗin...
"Ke Lantai ki yi abin da ke gabanki ban san surutu." Cewar Inna Kande.
Ai kuwa wani ya daka mata tsawa sai da ta tuntsire daga yadda take .
Musa ya kalli Lantai da yanayin tsoro yace, "Tabbas kin ban labari amma ban wajen ban san ko suwaye ba Lantai."
Ta taɓe bakinta ta dubi Barbushe ta ce, "Ni fa na yafe masu ma amma ka ce su dinga zuwa nan ina karanta masu labarin Jarumi Nasimat Yayana i dai kama sona."
Barbushe ya ja tsaki yace, "Gaskiya Nuratu ki bari na farke cikin ko mutum goma ne kawai sai zuciyata tai sanyi domin ganin hawayenki yasa jini nake so kawai ya kwarara yau."
Mai gari yayi wuf yace, "Kai haƙuri tunda magana ce ta zubar jini bari a fito da kaji a yanka maka, ai duk jini dai jini ne yaron kirki irin albarka."
Lantai ta tuno yadda mai gari ke ƙwamushe dabbobin mutane yace a ba shi kyauta duk damina wai yana da abincin gona babu masu ci.
Sai karaf ta ce, "Yayana su sauran su kawo mana kajin shi kuwa ya bamu Tumakai biyar Akuya biyar raguna kuwa tunda sun fi yawa ya baka biyar yaban biyar ladar zuwanka sai ya ba sauran ko da guda-guda ne kajin kuwa sai dai aita kamowa har a samu ko da ashirin ne ."
Mai gari yayi tsit yana jin yadda Lantai ta tsiyata shi lokaci guda.
Barbushe ya daka masu tsawa, "Ba ku ji abin da ƙanwata ke son ayi ba ne wai ?
Sai kowa ya miƙe yana kakkaɓe riga Hure sai sauri take tabar wajen Lantai ta kira sunanta.
Da farko harga Allah Hure tayi niyyar rugawa amma data waigo taga kwari da baka sai ta juyo tana kukan yara "Wayyo Innata wayyo Babana!
Barbushe ya kife ta da mari sai data saki fitsari don azaba.
"Ke ubanwa ke gareki da har kika aikata hakan ga ƙanwata ne?
To mu je yanzu ki soya ƙosan ki cinye ki shanye man don mai ...
Yaran suka amshe.
"Cau-cau maigida."
Hure tai ta bada haƙuri kamar ranta zai fice sai da Lantai ta tabbatar da Hure mai sunanta taji zata razana sannan ta ce, "Yayana ƙyaleta ai ba zata sake ƙosan ba Inna Kande zata dinga yi daga yau ."
Hure ta ce "Wallahi na amince ba zan sake saida ƙosai ba Lantai nayi nadamar abin da nayi ki yi haƙuri nayi nadama."
Da ƙyar Hure ta samu Lantai ta barta ta kwasa da gudu ta nufi gidanta tana jin cewa duk inda taga mai suna Lantai ita zata nemi sulhu kafin komi ya haɗa su ma.
Nan da nan sai ga kaji agwagi an tara su kamar kasuwarsu kawai wajen.
Lantai ta ce yaran Barbushe su shiga gidan kiwon mai gari su zaɓo manyan Tumakai da Awakai duk kazar da aka gani a kamota.
Haka kuwa akai sai ga mai gari ya tashi da Awakai basu wuce uku ba duk Lantai ta raba hada mutanen gari dai duk ta ba kyautarsu.
Barbushe ya tabbatar masu da duk Asabar da Lahadi duk wanda bai zo ba zai je da kansa ya ɗaukosa har gidansa.
Lantai farin ciki kamar tai hauka haka take ji.
So take labarin shahara da baiwar da jarumi Nasimat yake da ita ta baibaye ko ina can gabama ƙauyensu Barbushe zata koma karantama littafin.
Mu je dai zuwa.
Haupha
managarciya