Idan Tinubu na da wayo ba zai tsaya takara a 2027 ba — Datti Baba-Ahmed
Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da kada ya sake neman takara a 2027 idan har yana da wayo a siyasa.
Baba-Ahmed, wanda ya bayyana a shirin siyasa na gidan Talabijin na Arise mai suna ‘Prime Time’ a ranar Juma’a, ya bayyana cewa lokacin Tinubu ya ƙare, yana mai cewa komai yana nan a fili ga shugaba Tinubu da jam’iyyarsa ta APC cewa za su sha kaye a 2027.
“Ina tsammanin Tinubu zai yi murabus idan har yana da irin wayon da ake ɗauka yana da shi a siyasa,” in ji Baba-Ahmed.
Jagoran LP ɗin ya kwatanta Tinubu da wata irin mashahuriyar dabara ta siyasa da ta kai shi ga shirya fitowar ‘yan takarar shugaban ƙasa tun daga 2007, “wanda ya ƙare da satar zaɓe a 2023.”
Ya ce, “Ya tsallake 2007 sannan cikin wasa ya sanya Atiku ya tsaya takara, ya sanya Ribadu da wani a 2011, ya kawo Buhari a 2015, Buhari ya ci zaɓe, ya sake tsallake 2019 sannan suka sace 2023. Idan yana da wayo sosai, komai yana nan a fili cewa zai sha kaye a 2027.”
Sai dai kuma tuni fadar shugaban kasa, ta bakin mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Sunday Dare ya mayar wa da Datti martani.
A wani sako da ya wallafa s shafin sa na X, Dare ya kwata-kwata maganar da Datti ya fada babu hikima a ciki.
managarciya