Idan na zama ɗan Majalisa zan samarwa Mata da Matasa sana’oin dogaro da kai---Bargan Gombe

Idan na zama ɗan Majalisa zan samarwa Mata da Matasa sana’oin dogaro da kai---Bargan Gombe

Daga Habu Rabeel, Gombe.

Alhaji Sadeeq Gidado, Bargan Gombe na farko kuma masanin tattalin arzikin kasa da ya jima yana karatun sa a kasar Indiya ya kuma yi fice wajen taimakon al’umma ya yanke shawarar tsayawa takarar kujerar dan majalisar jihar Gombe da zai wakilci Gombe ta arewa bisa kudurin ci gaba da inganta rayuwar Mata da Matasa.

Sadeeq Gidado,matashi ne mai kishin al’umma yace ya yanke shawarin yin takara ne dan ceto mazabar sa ta Gombe ta arewa a majalisar tsara dokokin jihar ta hanyar tallafawa Mata da Matasa idan yaci zabe a shekarar 2023.

Bargan Gombe ya bayyana hakan ne jim kadan da kaddamar da kan sa a matsayin dan takarar kujerar majalisar Dokoki inda yace muddin aka zabe shi zai yi amfani da basirar sa na sanin sha’anin kudi wajen ingatna hanyoyin samarwa da jihar Gombe kudin shiga ba tare an musgunawa talakawa ba kuma zai cire musu kitse a wuta.

Mazabar ta shi ta kunshi unguwanni shida a fadar jihar da suka hada da unguwarBajoga da Dawaki da Shamaki da Nasarawo da Ajiya da kuma Herwagana, inda yace da yardar Allah ida jama’ar suka zabe shi zai ciyar da yankunan gaba.

Yace a matsayin sa na wanda ya zaga wasu kasashen duniya musamman Indiya da sauran su yaga yadda ake gudanar da al’amuran ci gaba zai hada kai da gwamnan sa ya da kuma kamfanoni da kungiyoyin da ya sani a can dan su hada kai a kawo wa jihar Gombe da mazabar sa abubuwan more rayuwa wanda talakawa za su amfana a dalilin sa.

 Alhaji Sadeeq Gidado, ya kara da cewa ita siyasa aba ce da aka samar da ita dan tallafawa al’umma amma yace yana mamakin yadda wasu ida suka ci zabe suke gujewa al’umma sai zabe ya kusa suke sake waiwayar su wanda hakan a cewar sa ba dai dai bane.

“Idan kuka zabe ni kamar yadda na alkawarta muku na tallafawa Mata da Matasa haka duk abunda zan gudanar sai na nemi shawarin ku kafin ayi idan baku gamsu da abunda zanyi ba zan hakura” Inji Bargan Gombe.

Ya yi amfani da wannan damar ya roki jam’iyyar sa ta PDP da ta duba cancantan yan takara wajen zaben fitar da gwani kar a bai wa masu zabe wato delegate  kudi su zabi wanda ba zai iya cin zabe a babban zabe na gama gari ba domin ko ta wane hali so suke su karya jam’iyya mai mulki ta APC.

Daga nan sai ya shawarci daukacin jama’a da cewa duk wanda ya kai shekara 18 kuma bai da katin zabe ya yi kokari ya yanki katin zabe domin duk yadda kake son mutum muddin baka da katin zabe ba za ka iya zabar sa ba.

xxx