Hukumomin Tsaro 7 Sun Karɓi Kyautar Motocin Aiki Sama da 100 Daga Gwamna

Hukumomin Tsaro 7 Sun Karɓi Kyautar Motocin Aiki Sama da 100 Daga Gwamna

 

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Laraba, ya mika motocin sintiri sama 100 kyauta ga hukumomin tsaro daban-daban na jihar, kamar yadda Tribune ta ruwaito. Hukumomin tsaro da suka amfana da kyautar motocin sun haɗa da ƴan sanda, sojoji, kwastam, gyaran hali, shige da fice da hukumar hana sha da fataucin kwayoyi (NDLEA).

Sauran hukumomin sun haɗa da rundunar haɗin guiwa da aka fi sani da Operation Burst, Amotekun da kuma hukumar kula da cunkoson ababen hawa ta jiha (OYRTMA). 
Gwamna Makinde na PDP ya ce gwamnatinsa ta kudiri aniyar taimaka wa jami'an tsaro wajen sauke nauyin da ke kansu ne duba da namijin kokarin da suka yi a sha'anin tsaro. Da yake ƙara musu ƙarfin guiwa domin jajircewa wajen magance dukkkan masu tada zaune tsaye, Makinde ya roƙi shugabannin hukumomin da kar su ji kunyar faɗa masa bukatunsu a koda yaushe. 
Da yake magana a madadin shugabannin hukumomin tsaro, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Adebola Hamzat, ya ce ya yi matukar mamakin yadda gwamnatin jihar ta ƙara raba masu motoci.