Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara za su rabawa mutane 600 tallafi

Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara za su rabawa mutane 600 tallafi

 

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal, Sakkwato.

Gwamnan Jihar Zamfara Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya ƙaddamar da ba da rabon kayan tallafi ga mata da matasa da sauran mabuƙata da yawan su ya kai mutum 600, ƙarƙashin jagorancin Hukumar Kula da tattara Zakka da Waqafi ta Jihar Zamfara. 

Wannan shirin ba da tallafi zai shafi mutum 450 da ýan kai da za su amfana da tallafin N30,000 don jarin ƙananan sana'o'i. Akwai kuma kimanin mutune 100 da ýan kai masu lalurar rashin lafiya da za su amfana da abinci mai gina jiki. 

Sauran sun hada da 60 da za su amfana da tallafin ɗaukar nauyin koyar da su karatu a fannin na'ura mai ƙwaƙwalwa. 

Yayin wannan ƙaddamar wa Gwamna ya ba da tabbacin cigaba da ba da muhimmiyar kulawa ga wannan Hukuma, bisa la'akari da irin mahimmancinta a cikin al'umma da ma addinin Musulunci.

Daga bisani, shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara Malam Abubakar Sodangi Algusawy, ya yi godiya.