Daga Mukhtar A. Halliru Tambuwal, Sakkwato .
A ƙoƙarin da Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato ke yi na inganta sha'anin karɓa da raba Zakka da Wakafi cikin kasa da wajen ta, wata tawaga daga Hukumar Zakka da Wakafi a Nijeriya ta samu halartar taron Waƙafi na duniya da ya gudana a kasar Pakistan karo na 10, da aka yi wa laƙabi da GWC 2022.
Tawagar jami'an Hukumar a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato) wanda shi ne Mataimakin Sakatare na Ƙungiyar Zakka ta Duniya, mai kula da ƙasashen Yammacin Afirika kuma shugaban riƙo na ƙungiyar Zakka da Waƙafi ta Najeriya (AZAWON).
Sadaukin Sakkwato ya jagoranci tawagar ne zuwa ƙasar Pakistan bisa gayyatar halartar taron Waƙafi da aka gabatar a farkon wannan watan ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na duniya da suka yi nazari kan batutuwa da dama da suka shafi Waƙafi a koyarwar addinin Musulunci.
Taron wanda ya gudana a Jami'ar lslamiyya, da ke Gundumar Bahawalpur, yankin Punjab a kudancin kasar Pakistan, ya mayar da hankali ne kan "Yadda za a yi amfani da Waƙafi akan sabon tsarin tattalin arziƙi da kuɗi a Musulunci.
Shugaban tawagar Nijeriya ya gabatar da maƙala a lokacin taron da kuma jawabin fatan alheri.
Shugaban ya bayyana cewa bada jimawa ba Jihar Sakkwato da ma Najeriya za su amfana da wasu muhimman abubuwan da aka tattauna akan su da suka shafi hada-hadar kuɗaɗen Musulunci, kasuwanci, kiwon lafiya, ilimi da sauran su.
Tawagar ta samu ziyarar wasu wurare don ɗaukar kwasa kwasai da cibiyoyin tarihi da al'adu da ilimi da kuma tattaunawa akan abubuwan da suka shafi Zakka da Waƙafi, kasuwanci, ilimi, lafiya, noma da sauran su.
Ma'aikatan da suka samu halartar taron sun nuna jin daɗin su akan samun wannan damar da ba da tabbacin aiwatar da horarwar da suka samu a cikin ayyukan su bayan sun koma gida.
Tuni dai tawagar Hukumar zakka da wakafi ta Jihar Sakkwato ta koma gida lafiya. a yayin da ta cigaba da kasancewa kan gaba wajen aiwatar da ayyukan karɓa da raba Zakka a arewacin ƙasar nan, da ma wasu kasashen duniya, inda masana suka tabbatar da cewa da a ce sauran jihohin arewacin ƙasar nan sun aiwatar da tsari irin na Sakkwato to, babu shakka da an yi maganin raɗaɗin talaucin da ake cewa yana damun yankin arewacin kasar nan, musamman idan masu kuɗin yankin suka fitar da Zakka ko suka bada Waƙafi kamar yadda Allah ya ce.