Hukumar zabe  ta bayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo

Hukumar zabe  ta bayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo da aka gudanar ranar Asabar.

An ayyana Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben bayan da aka kada kuri'u mafi yawa a zaben.

Gwamna mai ci ya fafata da Ajayi Agboola na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Olorunfemi Festus na Labour Party, LP, da Abbas Mimiko na Zenith Labour Party, ZLP, da sauransu, a zaben ranar Asabar.

Daga Abbakar Aleeyu Anache