Daga Ali Rabiu Ali, Jigawa
Hukumar kula da share filayan aikin noma ta kasa NALDA a karkashin ofishin Mai girma Shugaban Kasar Nigeria domin wadata kasa da abinci tanayin kokarinta domin samarda sakamako mai nagarta ta fuskar inganta aikin gona da kuma samar da abinci domin ganin an cheto jama'ar kasa daga kangin karancin abinci.
Kamar yadda bincike yanuna, hukumar NALDA tana yin aiyukan bunkasa harkar noma a fadin Nigeria da nufin karawa manoma kwarin gwiwa domin su rungumi aikin gona gadan - gadan. Wannan yahada da shigowa da matasa dakuma mata musamman mazauna yankunan karkara.
Bugu da kari, hukumar NALDA tana taimakawa kananan manoma harma da manyan manoma da kayayyakin aikin gona namusamman da nufin bunkasa harkokin aikin gona a fadin Nigeria domin ganin cewa nanoma sunkai ga samun nasarar da akeda bukata musamman tayanda manoman zasu zamo masu dogaro da kansu a koda yaushe.
Kamar yadda hukumar ta himmatu da cewa yin hakane kawai mafita wajen samun bunkasar tattalin azzikin kasa, kuma yazamana sukansu manoman sun samu kudin shiga dazasu iya dogaro da kansu ta fuskar aikin gona.
Irin taimakon da gwamnatin tarayya take baiwa manoma kai tsaye a karkashin hukumar share filayan noma ta NALDA yanada matukar armashi a yankunan karkara, hakan yasa hukumar NALDA ta kaddamar da gonakin gwaji ayankunan karkara da nufin fadakar da mutanen karkara akan irin damar dasuke da ita a bangaran aikin gona.
Bugu da kari, NALDA tana baiwa manoman horo, hakanne zai bawa mata damar kafa kungiyoyin 'Mata' manoma ayankunan karkara da Kuma fadakar da mutane akarkashin shirin mukoma gona.
Sakamakon hakane yasa wannan hukumar ta kafa makarantar da zata rika baiwa su manoman horo akan dubarun aikin noma yayinda suma wadanda suka sami horon kuma suka kware zasu samu damar horas da wasu domin ganin ankai ga nasara akan irin aiyukan da ita hukumar tasanya agabanta.
Samar da makarantar zai taimaka matuka sosai wajan horas da manoma dakuma gudanar da duk wasu shirye-shirye wanda hukumar takeyi cikin sauki musamman wajan baiwa y'an "saa - kai" (volunteer) da sauran manoma bita akan aikin gona cikin sauki.
Yayin da yakewa ganawa da manema labarai agameda wani taron da hukumar ta shirya na masu ruwa da tsaki a garin "SUDUJE" cikin Jihar Katsina, Bello Umar Kazaure kuma babban jami'in hukumar mai kulada Arewa maso Yamma (Northwest) yafadi irin aiyukan da hukumar NALDA take aiwatarwa awasu sassa na kasar Nigeria.
Yafada cewar katafariyar gona maisuna "Integrated Organic Farm Estate" a Jihar Katsina, ansamar da itane domin kyakkyawan zaton cewa matasa da mata na wannan jihar ta Katsina zasu samu ilimi da dubaru na musamman wajen koyon sana'ar aikin gona musamman a bangaren harkar kiwon kaji masu kwai da nama, kiwon kifi, kiwon zuma, kiwon dabbobi na shanu da tumaki.
Haka kuma da koyon aikin sarrafa kayan amfanin gona (product drying and processing) dakuma dubarun sayar dasu a harkan kasuwa irin ta zamani (offtaking).
Haka zalika, Kazaure yayi karin bayani akan wani aikin na musamman watau aikin ban'ruwa wanda aka samarda da injina masu amfani da hasken rana (solar irrigation) a garin "Daberam" , cikin karamar hukumar Daura a Jihar Katsina. A nasa jawabin dai, Kazaure yace hukumar ta NALDA tana kara jan hankalin manoman rani a "Daberam" da suyi amfani da wadannan injina masu amfani da hasken rana domin cigabansu a harkar aikin noma.
Yakuma zama wajibi cewa manoma su tabbatar da dorewar wannan katafaren aikin domin samun biyan bukatarsu tareda samarda kungiya wadda zata chigaba da gudanar da aikache aikachenta a karkashin kulawar shugabannin hukumar NALDA na jihar Katsina.
NALDA zata chigaba da iyakacin bakin kokarinta wajen ganin ta chika dukkananin alkawarinta musamman wanda suke gabanta domin chigaban manoma.
Yakara da cewar, kadan daga cikin irin ayyukan da hukumar zata gudanar sun hada da koyar da dadabarun aikin gona na zamani wanda duniya take alfahari dashi.
Wannan yahada da yadda za'a koyawa manoma komai tun daga tushe har zuwa karshe.
Yayin karatu a mataki na farko a makarantar da aka kafa din, za'a farane da takardar shaidar karamar Diploma wato ND abangaran fannin aikin gona, sauran kwasa-kwasan, sun hada da National Diploma (ND) ta kimiyyan aikin gona da kiwo (Agricultural Technology & Animal Production) da Diploma akan kiwon lafiya (Diploma in Health Technology).
Haka zalika, makarantar zata bada horo akan dabarun hannu abangaran aikin gona, kuma an amince da kwalin shaidar karatunsu afadin tarayyar kasarnan batareda nuna bambamchi ba.
Tuni, anyi tanadin dukkannin kayayyakin gwaji domin anfanin dalibai alokacin Practical domin daliban wanda suka hada da wajan koyan kiwon kifi da sauransu.
Yayinda jami'in hulda da hukumar (consultant) kuma masani akan fannin ilimi na KLM & KHALS da yake aiki da hukumar ta NALDA, Mr Samuel Ono yakara da cewa su al'ummar Jihohin Abia , Ogun, Katsina da Borno ne zasufi amfana da alkairin wannan makarantun da hukumar NALDA ta samar a Jihohin nasu.
Yakuma bukaci wadanda shirin zai shafa kaitsaye acikin wadannan wurare dasu rungumi shirin da hannu biyu domin ganin irin muhinmancin da shirin yake kunshe dashi.
Yakuma bukacesu da akalla su dauki nauyin karatun dalibai biyar biyar na iyalansu a duk shekara domin hakan zai taimaka wajan rage zaman banza kuma matasa da dama zasu zama masu dogaro da kansu agaba.
Haka zalika ya bukaci al,ummar Jihar Katsina amatsayinsu na masu masaukin baki a yayin taron dasu taimakawa hukumar NALDA wajan shawarwarin da yakamata domin tsarin yasamu nasara.
Saboda haka, ya kamata su taimaka wajan baiwa mazauna karkara musamman matasan su damar shiga adama dasu a cikin wannan harkokin na noma da hukumar ta kawo a Jihar tasu.
Yazama wajibi matasan su tashi tsaye wajan neman ilimi musamman a wannan makarantar da hukumar ta bude a Jihar domin amfaninsu domin suzama mutane na gari wanda al'ummarsu zasuyi alfahari dasu.