Daga Habu Rabeel, Gombe
Hukumar kare yancin dan adam ta kasa (National Human Right Commission) NHRC mai ofis a Gombe, ta sha alwashin yin hadaka da kungiyar jami’an tsaron sirri na farin kaya (Searchlight Private detective of Nigeria) (SPDN) wajen taimakon al’umma.
Shugaban hukumar ta NHRC a jihar Gombe Barista Mohamamed Shamsudden Ayuba, ne ya bayyana hakan a lokacin da tawagar hukumar suka ziyarci ofishin SPDN a Gombe dan neman hadin kai wajen tafiya tare dan gudanar da aikin su na kwatowa marasa gata hakkin su da aka danne.
Barista Mohammed Shamsudden, yace hukumar kare yancin dan adam gwamnatin tarayya ce ta kafa ta domin kare yancin al’umma kyauta ba tare da karbar kudi a hannun su ba, yace duk wanda aka zalunta ko aka takewa hakki zai iya zuwa hukumar ya shigar da korafin sa dan bi masa kadu.
Yace akwai wasu mutane da suke bude ofis barkatai suna kiran kansu human right suna karbar kudi a hannun al’umma wadannan ba hukumar kare yancin dan adam da gwamnatin tarayya ta kafa bane, kuma muddin suka kama irin su za su dauki mataki akai.
Sannan ya yabawa kungiyar SPDN bisa irin kokarin da suke yi wajen gudanar da ayyukan su na tattara bayanan sirri da kuma aikin sasanta al’umma wanda a wannan bangaren aikin yana kamanceceniya.
Shugaban hukuma ya yi alkawarin cewa a duk lokacin da kungiyar SPDN ta shirya za su bai wa mambobin su horo a bangaren kare hakkin dan adam ta inda aikin nasu yake da nasaba sannan su basu takardu da za su taimaka musu wajen kara gane yadda aikin yake a ilman ce .
Da yake mayar da jawabi kwanturolan kungiyar na SPDN na jihar Gombe Alhaji Rabilu Abubakar yabawa hukumar kare yancin dan adam din ya yi bisa wannan ziyara da suka kawo musu, sannan ya musu alkawarin yin hadakar idan bukatar hakan ta taso.
Kwanturolan yace ita kungiyar Searchlight Private detective of Nigeria kungiya ce mai zaman kanta da aka mata rijista daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya take kuma da rijista da hukumar nan mai yiwa kamfanoni da kungiyoyi ta CAC rijista da take da lambar rijista CAC/IT/NO.66748, kuma suka samu horo a bangaren tsaro da tattara bayanan sirri, yace kuma suna da hadin guiwa da dukkan hukumomin jami’an tsaro.
Daga nan sai yace su jami’an tsaro ne na sirri da suke aiki kafada da kafada da duk wani jami’in tsaro inda suke samar da bayyanan sirri su kuma jami’an tsaro su dauki matakin kare faruwar al’amarin kafin ya faru.
.