Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta gabatar da sabbin tsare-tsare da ƙa’idojin da za a yi amfani da su wajen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 ga Gwamnatin Jihar Kebbi.
Tawagar hukumar ce ta gabatar da sabbin tsare-tsaren a yayin wata ziyarar aiki da ta kai fadar Gwamnatin Jihar Kebbi a ranar Laraba, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Muhammad Bin Usman.
Daga cikin muhimman sabbin ƙa’idojin da hukumar ta bayyana akwai waɗanda suka shafi lafiyar mahajjata, inda ta ce an ƙara wasu nau’o’in cututtuka cikin jerin cututtukan da ba za a amince wa masu ɗauke da su su tafi aikin Hajji ba.
Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani likita da aka tabbatar da cewa ya sanya hannu ko ya amince da tafiyar mahajjacin da ke ɗauke da ɗaya daga cikin cututtukan da ba a yarda da masu ɗauke da su su je aikin Hajji ba, zai fuskanci matakin hukunci.
A cewar NAHCON, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya sun tafi aikin Hajji cikin ƙoshin lafiya, tare da rage matsalolin lafiya da ka iya tasowa yayin gudanar da ibadar a ƙasa mai tsarki.
Hukumar ta kuma bayyana gamsuwarta da yadda Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi ke gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji, tana mai cewa jihar na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi nisa wajen shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2027.
NAHCON ta ce ci gaba da tattaunawa da hukumomin jihohi da hukumomin jin daɗin alhazai na da muhimmanci wajen tabbatar da samun ingantaccen tsari da kuma nasarar aikin Hajjin shekarar 2027






