Hukumar INEC Ta Dage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisun Jihohi

Hukumar INEC Ta Dage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisun Jihohi

 
Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta kammala duk wasu shirye-shirye na ɗaga zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi wanda za'a gudanar ranar 11 ga watan Maris. 
A halin yanzun INEC ta ƙara mako ɗaya, zaben ya koma ranar 18 ga watan Maris, 2023, wata sahihiyar majiya a hukumar ta faɗa wa Daily Trust. Bayanai sun nuna cewa an ɗage ranar zaben ne sakamakon gazawar INEC na sake saita na'urorin BVAS da aka yi amfani da su a zaben da ya gabata, domin sake amfani da su a karo na biyu. 
Majiyoyi masu alaƙa da batun sun bayyana cewa yanzu haka shugabannin INEC na taro domin duba yuwuwar ɗaga zaɓen zuwa 18 ko 25 ga watan Maris, 2023. Sai dai alamu sun nuna jagororin hukumar sun raja'a kan ƙara mako ɗaya, watau maida zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023.