Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa a Jihar Katsina ta cafke wani mutum da ake zargi da yunkurin lalata da wata mata bayan ya yi mata alkawarin dinka mata kayan Sallah tare da ƴaƴanta.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Abdullahi Salihu Almujawwid na sashen kula da kafafen sadarwa na Hukumar Hisbah ta Batagarawa ya fitar.
Sanarwar ta ce mutumin ya yi alkawarin taimaka wa matar da kayan Sallah da ita da ƴaƴanta, amma daga baya ya yi kokarin amfani da wannan damar wajen neman lalata da ita.
Sanarwar ta kara da cewa bayan samun rahoto, jami’an Hisbah karkashin jagorancin Kwamanda Malam Sadiq Ibrahim Gyaza sun bi diddigin lamarin inda suka cafke wanda ake zargin kafin ya aiwatar da abin da ake zarginsa da shiryawa.
Sanarwar ta kuma ce kwamandan Hisbah na Batagarawa ya yi kira ga al’umma musamman mata da su yi taka tsantsan da duk wani da ke neman amfani da sunan taimako domin yaudarar jama’a.





