How To Make French Rice
Abubuwan da ake bukata:
Shinkafa
Nama
Tumatir
Tattasai
Albasa
Tarugu
Maggie
Eggs
Oil/bluebnd
Carrots
Green beans
Oven
Yanda ake hadawa: zaki dafa Naman ki tare da spicy, ki dafa shinkafa kaman perboiled ya dahu kadan, Sai ki yayyanka tattasai da albasa da tumatur da carrot tarugu, sannan ki dauko Naman ki yayyanka shi kanana.
Sai ki juye shinkafan ki cikin kwani Mai fadi, ki saka maggi da ruwan Naman da kika dafa, da curry zaki hada kaman hadin dambu, har mangyada ki saka da Naman da kika yayyanka, sai ki dauko try din oven din ki, ki juye shinkafan kan try din oven, ki dauko tattasai da albasa da tumatur ki jera kan shinkafan, da carrot din ki duk ki jera.
Sai ki dauko egg din ki fasa shi cikin kwano daban ki zuba kan shinkafan ki tabbata egg din ya ishe shi sosai,saboda Kwan ne zai sa ya fito kaman waina.
Sai ki tura cikin oven ki Kunna 30 to 35 minutes. Idan ya dahu Sai ki sauke ki yanka shi. Ki Dora kan plate. Ready to serve.
Safiya Usman
managarciya