How To Make a Special Spring rolls

How To Make a Special Spring rolls
 
Abubuwan da ake bukata
 
Filawa
Nama
Cabbage
Tattasa/albasa
Maggi
Gishiri
 Nonstick frying pan
Brush
 
Yanda zaki hada: zaki tafasa nama tare da kayan dandano ya dahu sosai Sai ki sauqe, ki jajjaga tattasai ki tafasa shi ya tsotse  ruwa ki aje gefe. Sai ki daka nama ya daku kaman zakiyi dambun Nama. Sai ki hada Naman tare da tattasai da albasa kisa maggi daidai dandanon ki.sai ki yayyanka cabbage ki zuba.
Sai ki dauko filawa  ki kwaba kwabin kunu amman kada yayi ruwa sosai. Sai ki Dora nonstick din ki kan wuta ki shafa kullun filawa da brush zaki ga ya taso Sai ki cire ki Dora kan try, Sai ki debo ingredients dinki na nama da cabbage Sai ki zuba. 
Zaki dauko rolling din daga sama ki rufe kaman rabi Sai ki kama gefe gefe Shima ki rufe Sai kiyi nadin tabarma. 
Haka zakiyi har ki kare. Sai ki soya ki nemi lemun ki danne da shi.
Tested nd trusted 
Daga Safiya Usman