Hon Sadiq Gidado Yayi Kira Ga mutanen Gombe Da Su Guji Sake Zaɓan APC A Jihar
Yayi wannan Kiran ne Yayin Tattaunawa da Gidan Radiyon Jewel FM Dake Garin Gombe
Hon Sadiq Gidado ( Bargan Gombe) Wanda ke Jagorancin Kungiyar 'Yan Takaran Majalisar jaha a Gombe wadanda Basu samu Nasarar zabe ba na Jamdiyar PDP
Tattaunawarsa Tsakaninsa da Danjarida Abdul'aziz sani labaran
Abdulaziz sani labaran ya Fara Tambaya da cewa
"Wannan dan Takaran naka Dakake ta Kodawa mutane suna maganar basusan Alkhairan sa ba a Jihar Gombe"?
Amsa: Eh Dalilin da yasa mutane bazasu san Alkhairansa ba shine Shiba mutum bane da yakeson yayi Abun Alhairi ko Taimako Aje ana yayatawa sabida yayi Imani Domin Allah yakeyi badon wani ya yabeshi ba
Yayi aiyuka na Taimako a wurare daban daban
Misali, Akwai Borhole da yayi mana a Anguwanmu bana shekaran Borhole din Takwas(8)
Bayan wannan yayi guda uku (3) A shamaki Ward da anguwan Bajoga
Kabar maganan tallafin karatu da yake bawa yara sannan bar maganan samawa yara aiki da yayi a Banking sector
Kaduba irin jami'ar kashere ai ya Gina musu hostel wannan dalibai suke amfana dashi.
Tambaya? "yanzu Fiskantan Gwamnati mai ci zakuyi ta Ina kake ganin nagartan Dan Takaran ku zai iya buge Gwamnati mai ci"?
Amsa: "Ai wannan Abune a Fili indai kata6a rike mukami Anan ne za'a Gane kai waye ne idan kadauki misali Gwamna da kake magana mai girma gwamna Inuwa Yahaya mutum ne Wanda ya dauki Alkawura da ya gagara cikasu
Tambaya? Hon. "Idan kalura anyi ayyuka a duk Gundumomi 114 kowani Gunduma yamata kilometer 11 na hanyoyi da Asibitoci
maizakace akan wannan"?
Amsa: Aiki Akayi KO Aika Aika? Saboda duk aikin da zakayi yaka mata kayi aikin da zai ta6a talaka kai Tsaye ne amma duk aikinda Gwamnatin nan tayi inason Tabbabatar Maka aikin ne na biyan bulatar Kai Domin su Gina kansu ba Talaka ba
Yace zai kawo Taki watan 'kaza' yakawo takin ne? Tunda yazo bai Rabawa Talakawa Taki ba
Kwangila da akace yana Bayarwa shima idan kadau keshi zakaga nasu suke bawa kuma akwai kwangilan da har yau ba'a fadi su waye suke kwangilar ba, wannan sannanen Abu ne
misali, kwangilan Gina katangan gidan kwamnati ba'a fadi kamfanin da take yin aikin ba
Kuma Gina Katanga kawai kusan Biliyan Biyu (2)
A wannan jahar kanada mutane da suna kwana da yunwa, talauchi, kana da mutanen da baka kawo musu taki ba da matasa basu da akin yi wanda ka hanasu ayyukansu su 5000 ka rabasu da ayyukansu
Ni yanxu haka Tausayin mutanen Gombe nakeyi yanzu haka saboda idan Ba'a dauki Mikati ba da YunKurin kawar da Gomnatin Nan ba za'asha wahala kwarai a Jihar Gombe
Shiyasa muke Kira Ga mutanen Gombe damu Zamubi Muhammad jibrin Dan Barde
Sabida Gomna meci Yana koikoyon Gomnan Kaduna ne jeka Katambayi abinda yafaru da Yan kasuwar Kaduna na yadda Gomnati ta rusa masu shaguna Kuma Yabasu Haya kaida shagonka Amma ka koma biyan Haya to abinda Gomna meci ke kokarin aikatawa a Gombe kenan yakamata yan kasuwar Jihar Gombe Dasu Farka
Tambaya: "katangan Government house kowa Yasani Mahdi ka ture kuma, ta fitar da jaha kunya ce"?
Amsa: "To muna duba alkawaruka da yayi kafin ya Hau mulki ne da kuma Abu buwa da yakeyi yanxu akan mulki
Shine yace zai samawa talaka sauki a Rayuwarsa to yanxu meye saukin da aka samawa talaka a harkan Gina katangan Government House
sannan hanyoyi da ake cewa yayi hanyace da zaka rusa gidan wani kuma kudinda zaka bashi KO fili bazai sayaba a anguwan KO bayan Gari
kaga wannan shiyasa kakega kashi 99% na mutane da hanya yabiyo ta Gidansu kuka sukeyi suna Allah wadai saboda basa bada Isheshen kudi,
Bazaka hada ba lokacin da Gwamnatin mu ta PDP Ke mulki ba Na Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo mutane Har Allah' Allah sukeyi kwalta yabiyo Kan Gidajensu
Tambaya: " Hon. Yanzu ga wani dan takara da yafito mai suna Raba Gardama Mezakace akan sa kuma Gashi yama raba motochi mezakace akwan matashin Dan Takaran nan"?
Amsa: " Toh kasan mu Gaskiya irin salon siyasar mu munfi maida hankali wajen fadan Alkhairan Dan takaranmu Domin mutane su tabbatar Dantakarar mu ya chanchanta.
Tambaya: "Meya baka karfin Guiwa Kake Ganin Zakuci Zabe"?
Amsa: " Babban abunda yabani kwarin Guiwa shine Jajircewan Dantakaranmu da kuma wannan shine kwarin guiwan mu kuma ganan Alkhairansa yanxu suna fitowa fili
Yan jahar gombe suna cikin wahala
kuma bugu da kari Abun takaici idan Natuna yadda harkan Sarakunan Gargajiya yakoma yanzu dalilin wannan Gomnatin kuma wannan bawan Allah kafin kaxama Gwamna sanda kaxo kace zaka Girmama su da kuma zaka musu adalci zaka daga darajarsu sannan yanzu kazo kana musu abunda kaga dama.
Shifa basarake duk kudinda zaka bashi muddin bazaka Girmamashi ba to Abanza ne
Tambayar karshe: " wani kira zakayi Ga mutanen Jihar Gombe musamman matasa Domin su zabi Dantakarku na Jamdiyar PDP?
Amsa: Ina kira Ga matasa bama su kadai ba duka mutanen Gombe mu maida hankali muzo mu hadu mu hada kanmu mu Zabi Muhammad Jibrin Danbarde domin shine zai Ciro mana kitse a wuta
Muta ne mu saka jahar Gombe a gaban mu fiye da abunda zamu samu mu saka a Aljihunmu Kwanan nan Yatara Pam. Secs. Yace su Barayi ne kunga wannan Baza'a a manta ba, KA duba Treasury House sanda yakoma kamar filin 9 yan makarantan primary duk kuma saka makon tsarin Dangwala yatsa (Tomprint)
Katafi nan Asinitin Bulkashuwa idan za'ayi Tiyata amma sai kaga Ana kunna candle Ko waya ana Haskawa
Dole mutanen Gombe su Bukachi Chanji Muna Kara Kira Ga Jama'a da Afito Kwai da Kwarkota a zabi PDP domin kawo sauyi a Jihar Gombe.
managarciya