Harkar Tsaro Zata Sami Kaso Mafi Tsoka A Kasafin Kudin 2022 --- Ahmad Lawan 

Harkar Tsaro Zata Sami Kaso Mafi Tsoka A Kasafin Kudin 2022 --- Ahmad Lawan 
Harkar Tsaro Zata Sami Kaso Mafi Tsoka A Kasafin Kudin 2022 --- Ahmad Lawan 
Daga Babsngida Bisallah, Minna
Shugaban majalisar dattawa,  Ahmad Lawan yace majalisar dokoki ta tarayya zata tabbatar an ware ma bangaren tsaro kaso mafi tsoka a kasafin kudin shekara mai zuwa dake gaban majalisar. 
Lawan yayi wannan bayanin ne a ranar Alhamis wajen bude taron mambobin kwamitocin tsaro na majalisun dokokin kasashen Afrika na 5 a Abuja. 
Shugaban majalisar ya gaya ma mahalarta taron cewa, "a yau kasar mu da nahiyar mu har ma da duniya baki daya na fuskantar kalubalen rashin tsaro. 
Mai ba shugaban majalisar dattawa shawara akan aikin jarida, Ola Awoniyi ne ya tabbatarwa manema labarai, a wata takardar manema labarai da ya sanyawa hannu.
Yace " A majalisar mu, kwamitocin mu na tsaro su suka fi kowane kwamiti fama da aiki. 
"Tun kafa kwamitocin a shekarar 2019, mun dauki lamarin rashin tsaro a matsayin wani bangaren na tsarin jadawalin aikin mu na majalisa. 
"Mun yi imani cewa dole mu shawo kan wannan kalubale idan ba haka ba yunkurin mu na samar da cigaba ba zai yiwuwa ba. 
"A yan watannin baya ne majalisar dokoki ta tarayya ta amince da kwaryakwaryan kasafin kudin sama da naira bilyan 900, wanda kashi 80 daga ciki, kwatankwacin sama da naira bilyan 800 aka sa su a bangaren tsaron kasar nan. 
"A yanzu ma, da yardar Allah mun kuduri maimaita hakan a cikin kasafin kudi na 2022 in da zamu tabbatar cewa bangaren tsaro ya samu kaso mafi tsoka don samar da tsaron rayukan jama'a da dukiyoyin su.