Harin 'Yan Bindiga: Sanata Lamido Ya Yi Kalamai Masu Zafi Ga Mahara A Yankin Gabascin Sakkwato 

Ya kudirci Kai maganar gaban majalisar dattawa domin kara fito da hanyoyin magance matsalar baki daya, "da zaran mun koma hutu zan gabatar da kudurori ga majalisa, kafin nan na yi zama da shugaban rundunar sojoji na kasa da mataimakin shugaban 'yan sanda Mai kula da aiyukkan 'yan sanda da sauran jami'an tsaro na zauna da su Kuma sun yi min alkawali

Harin 'Yan Bindiga: Sanata Lamido Ya Yi Kalamai Masu Zafi Ga Mahara A Yankin Gabascin Sakkwato 
Sanata Ibrahim Lamido Wanda yake wakiltar Gabascin Sakkwato ya jajantawa mutanen garin Giyawa dake karamar hukumar Goronyo kan harin da aka Kai masu a Jumu'a data gabata da ya yi sanadin mutuwar mutum 4 aka yi garkuwa da mutum 7, da kuma Karamar hukumar Illela da aka kashe mutum daya.
A hirarsa da manema labarai cikin damuwa Sanatan ya mika sakon jaje amadadin kansa da  jagoran tafiyarsu waton Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ga mutanen jihar Sakkwato baki daya kan wannan harin da aka kaiwa mutane ba su ji ba su gani ba.
Sanata Ibrahim Lamido ya ce suna matukar kokarin ganin wannan lamarin na rashin tsaro ya tafi baki daya, hakan ya sanya ya yi zama na musamman da shugaban rundunar sojoji na Nijeriya abubuwan da suka tattauna yana da yakinin nan ba da jimawa ba matsalar za ta zama tarihi da ikon Allah.
Dan majalisar ya ce duk shugaba nagari nason koyaushe jama'arsa su zauna lafiya, cikin walwala hakan kawai zai samar da cigaba.
Ya nuna bacin ransa yanda yankinsa yake cikin damuwa da tashin hankalin rashin tsaro "in kana wakiltar jama'a kulum burinka su zama cikin farinciki, yanzu an Kai mutanen da muke wakilta suna cikin tashin hankali da fargaba.
"Ina jajantawa mutanen Giyawa da Goronyo da Gabascin Sakkwato da jiha baki daya amadadina da jagoran tafiyarmu Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Muna jajantawa dukan al'umma da matsalar tsaro ta shafa, Wallahi Allah ne shedarmu muna kan iyakar kokarinmu Kuma ba za mu tsaya ba har sai an samu nasara.
"Matakin da muke dauka Wanda muke son kawar da matsalar tsaro ta tafi gaba daya ne ba wai taje dan Wani lokaci ta dawo ba, matsalar tsaro ba abu ba ne da ake fadi a kafofin yada labarai, amma ina sanar da al'ummar Sakkwato ta gabas da yardar Allah zamu kai wannan matsalar karshe, bayan motocin da Mai girma Gwamna ya saye don yakar 'yan bindiga akwai shiraruwa da ba za mu sanar da duniya ba, amma tabbaci da ikon Allah abin ya kusa kai karshe," a cewar Lamido.
Sanata ya yi alwashin tallafawa iyalan wadanda harin ya shafa a matsayinsa na Sanata mai wakltarsu ya yi nasa shiri Yana kuma bayar da tabbacin gwamnati za ta yi nata shiri domin yi masu abin da zai sanyaya masu don duk Wanda ya rasa mahaifi ko mahaifiya ko Miji ko Wani na jini radadi ne da baya warkewa a zuciya.
Ya kudirci Kai maganar gaban majalisar dattawa domin kara fito da hanyoyin magance matsalar baki daya, "da zaran mun koma hutu zan gabatar da kudurori ga majalisa, kafin nan na yi zama da shugaban rundunar sojoji na kasa da mataimakin shugaban 'yan sanda Mai kula da aiyukkan 'yan sanda da sauran jami'an tsaro na zauna da su Kuma sun yi min alkawali.
"Hankalinmu ba a kwance yake ba nutsuwa ta gushe mana gaba daya, ba za ka so mutanen da kake wakilta ba su iya kwana gidajensu, ka ga Kai kwana a gidanka baya da amfani, ka sani na sani Allah zai tambaye mu ba za mu yi wasa da harkar rashin tsaro ba, masu tayarda kayar ban ai Suma mutane ne za mu yi nasara kansu da iKon Allah"
Sanata ya godewa kokarin gwamnatin jiha karkashin Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya Kuma jajantawa wadanda lamarin harin 'yan Bindiga ya shafa.