Harin NDA zai karawa sojojin Nijeriya kaimin murkushe 'yan ta'adda---Buhari

Harin NDA zai karawa sojojin Nijeriya kaimin murkushe 'yan ta'adda---Buhari
Harin NDA zai karawa sojojin Nijeriya kaimin murkushe 'yan ta'adda---Buhari
 
Harin da aka kaddamar akan ginin Makarantar Horon Soji ta NDA a ranar Talata, a maimakon ya sanyaya gwiwa kan irin hazakan Jami'an Sojin mu kamar yadda maharan suka so, zai kara azamar ga aniyar dake nan don kawo karshen aiyukan Ash-sha a Ƙasar, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka. 
 
Ya nunar da cewa farmakin, wanda ya yi sanadin rashin rayuka, ya zo a daidai lokacin da Sojoji suka sanya masu tayar da  kayar baya a gaba, irinsu  Ɓarayin daji, Masu garkuwa da Mutane da Sauran nau'in masu aika-aika ja da baya. 
Shugaba ya nuna za a dauki mataki a kankanen lokacin a gama da mutanen.
 
Ya jajanta wa iyalan wadanda   suka rasu  ya yi addu'a Allah ya ji kan su. 
Shugaba Buhari ya sha alwashin cewa, Rayukkan da aka salwanta  ba za su tafi haka kawai ba, akwai Sakayya na wannan Mumunar aikinsu, wanda daga bisani zai tsaftace halin damuwa da kasar ke ciki. 
 
Shugaban Ƙasa ya godewa 'yan Nijeriya wadan da ke ganin  kokarin sojojinmu, da jan hankalin masu Mumunar Siyasar tsana da su guji wannan aikin, ya nuna cewa, in banda masu iza wutar al'amarin, wannan lokaci ne da duk masu ƙishin ƙasa, da mutane masu fatan Alkhairi, zasu goyi baya da karfafa gwiwa ga wadan-da ke sahun gaba, don yaki da Mugunyar aiki a doron kasa.