Harin Jirgin Kasa: Ya kara fito Da Rashin Iya Shugabanci Na Jam'iyar APC A Nijeriya---Tambuwal

Harin Jirgin Kasa: Ya kara fito Da Rashin Iya Shugabanci Na Jam'iyar APC A Nijeriya---Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal amadadin gwamnati da jama'ar Sakkwato ya jajantawa gwamnati da mutanen jihar Kaduna kan harin da 'yan bindiga suka kaiwa jirgin kasa in da suka kwashe sama da awa biyu suna cin karensu ba babbaka saman fasinjoji fiye da 900 da aka dauko daga Abuja za a kaisu Kaduna.

 
A bayanin da gwamnan ya sanya masa hannu da kansa ya nuna kaduwarsa ga faruwar lamarin ya ce hakan ya kara fito da rashin iya shugabanci da jam'iyar APC ke yi a Nijeriya, "wannan lamarin da yake faruwa a baya ana ganinsa ne kawai a cikin fim da wasannin kwaikwayo sai ga shi yana faruwa a fili a cikin gwamnatin da mafi yawan 'yan Nijeriya suka ba ta dama," a cewar Tambuwal
 
Gwamnan ya ce jajantawa da zuwa wurin da lamarin ya faru bai isa ba kawai dole ne gwamnati ta tashi tsaye ta kula da hakkinta tare da baiwa 'yan kasa hakuri.