Hanyoyin Kariya da Maganin Kwalara
KIYON LAFIYA
CUTAR KWALARA
Dr. Asma’u Suleiman Galadima
Cutar kwalara, cuta ce ta gudawa (zawayi) da amai mai tsanani da kan iya halaka
mutum kai tsaye cikin ‘yan sa’o’i kalilan, idan har ba’a dauki matakin magani
ba. Ana samun cutar kwalara sanadiyar wata kwayar halitta da ake kira Vibrio choler.
Cin gurbataccen abinci ko ruwan sha maras tsabta, mai dauke da wannan kwayar halitta ne ke haddasa cutar. Haka kuma cutar ba ta da kaidi, takan kama manya da kuma kananan yara. Sai dai ta kan fi tsananta ko illa ga kananan yara.
ALAMOMIN KAMUWA DA CUTAR KWALARA
Gudawa Rashin ruwan jiki
Zawayi Fadawar idanu
Kasala Matsalar numfashi
Amai ko haraswa Bushewar baki
Tamukewar tafin hannu da kafafu.
MATAKIN FARKO NA MAGANCE CUTAR KWALARA
Yin Amfani da hadaden ruwan gishiri da sukari domin shayar da marar lafiya
YADDA AKE HADA RUWAN GISHIRI DA SUKARI DA KUMA YADDA AKE BA DA SHI
A sami tafasasshin rowan zafi, ko ruwa masu tsabta kimanin kwalba biyu na lemun kwalba, ko duk wani kwalba mai ma’aunin (60cl), Sai a zuba karamin cokali goma na sukari a cikin ruwan, sai a zuba karamin cokali daya na gishiri a cikin ruwan, Sai a cudanye (gwaraye) sosai da cokali, a rika bayar wa da cokali ko kofi a kowace safiya. Ana bukatar a hada wasu sabbin ruwan gishiri da sukari ba tare da anyi amfani da na jiya ba(wadan da suka kwana).
A dakatar da amfani da ruwan gishirn da sukari da zaran gudanawar (zawayin) ya
dauke. Ana bukatar a gaggauta kai marar lafiya asibiti mafi kusa idan har ba’a ga
alamar sauki ba.
Ku tuna ana bukatar a baiwa marar lafiya abinci mai ruwa-ruwa,
kamar kamu/Kunu ko ruwan dawo (ruwan da aka dafa fura) ko ruwan shinkafa.
YADDA ZA’A KAUCEWA KAMUWA DA KWAYOYIN CUTAR KWALARA
- A rinka tafasa duk ruwan da aka debo daga rijiya ko korama ko kuma gulbi.
- A tabbatar da tsabtar jiki da muhalli a ko yaushe.
- Haka kuma a tabbata an wanke hannaye da sabulu idan an fito daga ba haya (ban daki)
- A tabbatar da an ci abinci ko abin sha tsabtatacce, hakanan kuma a kiyaye tsabtar wurin shirya abinci, kuma a tabbatar da cewa abincin ya dafu sosai kuma bai lalace ko ya rube ba kafin a ci.
- A rika neman shawarwarin malaman kiwon lafiya a koda yaushe.
Dr. Asma’u Suleiman Galadima
managarciya