Halin Da Sakkwato Ke Ciki Bayan Sanya Dokar Hana Fita
Dokar ta baci ta awa 24 ba fita da gwamnan Sakkkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sanya a jiya Assabar saboda tashin hankali da ya barke a wasu sassan jihar in da aka fara kone-kone da sace-sace, bayan kammala zanga-zangar lumana da aka gudanar domin kira ga jami’an ‘yan sanda su saki wadanda suka kama da zargin Kashe Daborah Samuel wadda ta zagi manzon Allah a ranar Alhamis data gabata.
Dokar ta soma aiki nan take, wayewar garin Lahadi an baza sojoji a manyan hanyoyin da suka fi matsala a birnin jihar, in da suke hana masu ababen hawa wucewa a ko’ina.
Wakilinmu ya zagaya a birnin jihar in da a tsarin dokar an raba birnin jihar biyu akwai wuraren da aka hana zirga-zirga da kuma wuraren da kowa yana sha’anin gabansa.
Titin Abdullahi Fodiyo da Ahmadu Bello da Sarki Yahaya da Aliyu Jodi da Titin Maiduguri da dukkan hanyoyin da za su hadaka da babbar kasuwa da babbar tashar mota da wadanda za su kai ka fadar Sarkin Musulmi dukkansu a rufe suke sojoji suna hana yawo samansu.
A gefen Unguwar Rogo da Minanata da Mabera da Nakasari da Tudunwada da sauransu, za ka samu mutane suna harkokinsu ba wata tsangwama ko kyara daga wurin jami’an tsaro.
Dokar ta awa 24 da ake sa ran wa’adinta zai cika karfe 6 na marece, jami’an tsaron za su kauce domin a fito a cigaba da harkoki cikin lumana ba tsangwamar juna, Sakkwatawa sun yi biyayya matuka ga wannan dokar domin ganin zaman lafiya ya dawo kamar yadda aka saba.
managarciya