Home Labarai Halin da mutanen ƙauye suke ciki  a Sakkwato ta sanya Malamin addini tsayawa takarar...

Halin da mutanen ƙauye suke ciki  a Sakkwato ta sanya Malamin addini tsayawa takarar Gwamna a 2027

8
0

Sanannen malamin addinin Musulunci a Sakkwato Malam Bashir Ahmad Sani da aka fi sani da Malam Bahar Ɗanfili ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Sakkwato a kakar zave mai zuwa ta 2027.

Malamin ya sanar da qudirin nasa a wurin tafsirin bana a birnin jiha ya ce yanke hukunci ya biyo bayan rangadin da ya yi ne a qauyukka 65 a faxin jihar Sakkwato domin ya samu qorafi da yawa na mutanen jiha.

A cewarsa mutane na buqatar xaukin gaggawa kan matsalar tsaro dake qara tavarvarewa da tsadar rayuwa dake addabar wasu magidanta a jiha.

“Shekara 22 muna yin wa’azi kan karantarwar addinin musulunci, ba mu tava zagin kowa ko kuma a ganmu cikin yekuwar zaven wata  jam’iya ba,” a cewarsa. 

Ya ce kun yi ta kira da mu yi takara muna cewa ba mu da sha’awar shiga siyasa kullum kuna yin kiran ina cewa a’a tau yanzu na karva.

Malamin bai ambaci jam’iyar da zai tsaya takara ba, a baya kafin nasarar wannan gwamnati ta Ahmad Aliyu suna da kyakkyawar alaqa da mutanen, bayyana qudirin nasa na nuna ba tafiya tare tsakaninsa da gwamnati mai ci ta APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here