Haɗuwar Sanusi Da Wike Baya Da Alaƙa Da Siyasa

Tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi ya kai ziyara a gidan gwamnatin jihar Rivers jim kaɗan bayan kammala taron Maulidin Sheikh AHMADU TIJJANI (RTA) na jihar Rivers dake kudancin Najeriya.

A yau ne Lahadi 03/10/2021 aka gudanar da Gaggarumin Mauludin SHEIKH AHMADU TIJJANI (RTA) a babban Filin wasa (Stadium) dake Hausa- line dake birnin Fatakwal na jihar Rivers.
Taron ya samu halartar tsohon sarkin kano mai Martaba KHALIFA SUNUSI LAMIDO SUNUSI (Khalifa Tijjaniyya na Najeriya) da Manyan Shuwagabannin Addinin musulunci da 'yan Agaji Fityanul Islam da Munazzama na sassa daban-daban daga Jihohin kudu maso kudu.
Zuwan Sarkin a gidan gwamnati ba ya da alaƙa da siyasa ziyara ce ta ban girma.