Haɗaka: Mun fara zawarcin gwamnan Zamfara - ADC
Jam’iyyar gamayyar ƴan adawa ta African Democratic Congress (ADC) reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara zawarcin gwamnan jihar, Dauda Lawal da sauran ƴan siyasa nagartattu a jihar domin su shiga jam’iyyar kafin babban zaɓen 2027.
Da ya ke magana da manema labarai a Gusau a jiya Juma’a, Shugaban jam’iyyar ADC na jihar, Kabiru Garba, ya bayyana cewa jam’iyyar ta karɓi sama da sabbin mambobi 100
Daga wasu jam’iyyu daban-daban cikin kwanaki goma da suka gabata, ya na mai bayyana sauyin sheƙa ɗin a matsayin babbar ƙarfafa wa jam’iyyar gwiwa da ƙima.
"Yanzu da na ke magana, fiye da mambobi 100 daga jam’iyyu daban-daban sun sauya sheƙa zuwa ADC a Zamfara cikin kwanaki goma da suka wuce,” in ji Garba.
Jaridar Daily Nigeria Hausa ta ruwaito cewa shugabn ya bayyana fatansa cewa ƙarin 'yan siyasa daga jam’iyyar APC da jam’iyyar PDP za su sauya sheƙa zuwa ADC a Zamfara nan ba da jimawa ba,
Ya na mai jaddada cewa jam’iyyar tana maraba da duk wanda ke da ɗabi’ar gaskiya a siyasa da kuma jajircewa wajen inganta shugabanci.
Meye Ra'ayin ku ga tuntubar jama'a zuwa Sabuwar Tafiya?
managarciya