HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa Fita Ta 38

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa Fita Ta 38

*HAƊIN ALLAH* 

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 


                 

                   Page 38

Daddy ya nisa ya kalle su duka ya ce, "Lokacin da na tabbatar da cewar Iyami ta sace min yarinya ta gudu da ita, sai najS tsani dangina na tsani ahalina tsanar gasken-gaske. Hakan yasa na tattara kayana baki ɗaya cikin dare na rubuta takarda na ajiye ma Yayana da mu ka je Lagos tare a lokacin.

Ban ji ina son sake rayuwa da kowa ba sai da ɗiyata Alawiyya don haka na tafi tashar mota kai tsaye na shiga motar Bauchi, ko a cikin motar ban da hawaye da takaici babu abin da nake yi, ace wai danginka sun yi maka tsakani da iyalinka? Wannan wace irin rayuwa ce mai wahalar gaske da babu imani babu tausayi balle zumunci? Haka na saka kaina cikin cinya na kama matse hawayen baƙin ciki.
Har muka isa Bauchi ban daina kukan baƙin ciki ba, haka kowa ya sauka ya kama gabansa aka barni zaune ina tunanin ta ina zan fara? Ga shi ba kuɗi gare Ni sosai ba, balle na samu gidan haya ko shago na bincika na kama.

A tasha na zauna tsawon lokaci sai ga wani dattijo ya yi min sallama, bayan mun gaisa ya ce min, "Yaro baƙo ne kai ko?" Na girgiza mai kai alamar e, na kuma buɗe bakina na gaya mai cewa, "Daga Lagos nake ina neman yarinyata da wata mata mai saida abinci inyamura mai suna Iyami ta gudo da ita, to matsalar ban san a wane gari take ba, na dai zaɓi zuwa nan ne don raina ya ban zan iya ganinta."
Mutumin ya kalle Ni ya nisa sosai ya ce, "To Yaro lamarinka akwai ban tausayi ka rasa yarinyarka kuma kana da tabbacin tana da rai kuma a hannun wadda babu hasken musulunci a tare da ita tabbas akwai matsala mai tare da tashin hankali. Don haka zan taimaka maka na kai ka gidana a kwai shago sai ka zauna a ciki har Allah Ya yi nashi ikon. Sai ka zauna a nan Insha Allah zaka dace indai kana raye tana raye to tabbas zaku haɗu wata rana."

Wannan bawan Allah shi ne ya ɗauke Ni ya kaini gidanshi ya ajiye Ni shagon gidan na ajiye kayana. Kasancewar ba wasu kuɗi a hannuna kuma ina don in fara sana'a ko da ba wata babba bace ba, kuma maigidan ya ɗauke min nauyin abin da zan ci insha yasa na nemi yaban shawarar sana'ar da zan fara yi a garin.

Muka zauna muka tattauna yaban shawarar na fara saida kayan gwanjo. Ba a ɗauki lokaci ba kuwa na fara saro kayan gwanjo ina kaiwa kasuwa abu kamar wasa sai ga kasuwar gwanjo ta amshe ni sosai har ta kai ko ba ranar kasuwa ba ina ajiye kayana a ƙofar shagona ina ciniki sosai kuma. Haka Allah Ya ɗaukaka Ni sosai a kan sana'ata .

Malam Lado shi ne mutumin da ya sauke Ni a gidansa, yana da mata guda da yara manya duk sun yi aure wasu maza wasu mata, akwai mata guda biyu dake zawarci a gidan da Safiya da Asma'u, Ni dai iyaka ta da su gaisuwa, sai idan sun ga kayan da suke so, su yi min magana Ni kuma zan ba su ba tare da na amshi kuɗin su ba, saboda mahaifinsu ya gama min komai tunda ya ban wajen zama yake ci da Ni kuma. Sai dai duk da haka Ni ma ranar kasuwa nakan yo cefane mai kyau na aika cikin gidan da su.

Ashe wai Safiya da Asma'u suna ta cacar bakin kowace sona take aure na za ta yi, Ni kuma babu wadda na taɓa nuna ina so ko da wasa a cikinsu, to Ni wace soyayya ko aure zan bayan an raba Ni da macen ƙwarai macen kirki Fatima? Sannan ga tunanin ɗiyata Alawiyya da kowace rana da shi nake kwana da shi nake tashi? Hakan yasa ko da na fara jiyo ƙamshin maganar sai na sake kame kaina sosai ban sakar masu fuska ko fitowa su kai ba ruwana da su, ba ko da yaushe nake amsar gaisuwar su ba.

Haka rayuwa tai ta juyawa a Bauchi ban da wata matsala sai ta abin da ya fito da Ni daga gida. 
Ranar wata Laraba tun da safe na jiyo makoki daga cikin gidan Malam Lado, ina shiga na samu labarin rasuwar shi da asubar fari. Nayi matuƙar baƙin ciki sosai naji babu daɗi, haka akai zaman makoki har na kwana bakwai, sai na fara haɗa kayana da zummar barin garin na koma wata Jahar ko Allah Ya ci da Ni da ganin Alawiyya.

Sai dai lokacin da na shiga gidan don nayi masu bankwana suka fasa kuka suka ce don Allah kar da nayi masu haka, Ni suke gani suna ɗebe kewar maigidan don Allah na cigaba da zamana inda nake har mai rabawa ta raba.

Ba don na amince da cewar zan rayu da su har mutuwa ba na amince na fasa tafiya sai don kar su ji babu daɗi a lokacin yasa na ajiye a raina zan ƙara zaman shekara guda sai ka ƙara gaba abina neman Alawiyya.

Bayan wata uku da mutuwar Malam Lado wata rana da dare ɓarayi suka zo shagona suka kwashe min komai su ka sassare Ni sosai sukai tafiyarsu.
To a nan fa na fara gane da suwa nake zaune. Domin kwata-kwata aka daina ban abinci daga gidan aka daina min duk wani abu na kyautatawa da aka saba yi min a gidan. Ƙarshe ma sai suka kira Ni suka ce idan ina son zama a shagon to na fara biyan kuɗin hayar shagon.
Nayi matuƙar mamaki sosai kan yadda lamarina da matan gidan ya juye, saboda ba wata mu'amala ta kirki dake wanzuwa a tsakaninmu da su sai gori da habaicin da suke fitowa ƙofar gidan suna sakarmin wai na zauna ba kunya ba tsoro ina cin abincin marayu ina zaune gidan marayu ban iya taɓuka abin sisi a cikin gidan.

Ni kuma ga Ni kwance sai jinyar raunuka nake dake jikina haka nake kwana na wuni ban ci komai ba sai fa idan wani ya zo ganina cikin abokan sana'ata ya ban wani abu nake amfani da su nake siyen abinci nake siyen magani. Haka na samu da ƙyar manyan raunikan dake jikina suka warke na ɗauki surutuna manya na kai kasuwa na saida na haɗa kuɗin na je gidan nayi masu bankwana da godiya na basu makullin shagon na ƙara gaba, ban tsaya ko'ina ba sai garin Zamfara.

A Zamfara ma nayi rayuwa mai wahalar gaske domin na isa ban da kuɗi kuma ban san kowa ba, kuma ban samu wanda ya taimake Ni ba, don haka a kasuwa na cigaba da rayuwa ta ina kwana cikin masallacin kasuwa nan nake rayuwa ina sana'ar dako da aikin gini da wanke mota ko mashin, sannu a hankali na fara haɗa kayan gyara kasancewar na iya gyara sosai na kama gyaran mota da mashin a cikin tashar, cikin ikon Allah na samu mutanen da suke kawo min gyara sosai sai ga Ni na maida kuɗaɗen da akai min fashi a garin Bauchi har da riba.

Sai ga Ni har da yarana waɗanda suke tayani aikin gyara a cikin tashar abun gwanin ban sha'awa, sai dai nakan shiga cikin gari na yi yawo sosai ina neman Alawiyya duk inda naga mai saida abinci inyamura sai na tambaye ta ko ta san wata mace mai saida abinci da tai zama a Lagos mai suna Iyami? Ban taɓa dacewa ba har Allah Ya kawo wata ƙaddarar ta afka min, ta wata motar baban Soja daya kawo gyara yaban makullin cikin dare ban ankara ba yarana ashe sun haɗa baki suka kwashe kayan motar masu muhimmanci suka gudu, daman ga shi  Ni da su duk ɗaya ne, basu da kowa a garin ka zo Na zo ne Ni da su baki ɗaya a garin.

Ai kuwa sojan ya ce bai yadda ba, ya turomin yaransa suka tafi da Ni barikin su babu wata irin azabar da basu yi min ba, ya ƙwace duk wata dukiyata ya kuma yi min azaba ta tsawon wata guda sannan ya sake Ni, lokacin ko tafiya ban iya yi tsabar wahala da na sha gun sojan nan yasa na fita hayyacina na koma kamar mahaukaci.
Haka na bar garin Zamfara wutsiya zage ba arziƙi ga Ni ban da komai ban da abin komai. 

A haka na samu na ji jinyar jikina na wahalar dana sha, na nemi taimakon kuɗin mota a masallacin da nake zaune a tashar na shiga motar Kaduna saboda naji ana cewa garin ya tara kowane irin yare musulmi da arna don haka sai na tafi can ko Allah zai sa na ga Alawiyya tunda Iyami arniya ce ba mamaki tana can tana cigaba da saida abincin tare da Alawiyya.

Zamana garin Kaduna da farko na sha wahala saboda rashin kuɗi da rashin sabo da garin yadda ya haɗa manyan hatsabibai manya da yara bariki iya bariki babu wanda ba a yi a garin Kaduna.

Sai kawai na dage da neman na kaina ta hanyar shiga aikin sauke siminti da nake duk rana ba fashi har na samu kuɗi masu yawa ba laifi na kama shagon da na dinga kwana tunda da a tasha nake kwana ƙasan motoci.

Sannu a hankali na cigaba da keman kuɗi kuma na dage da zuwa duk inda naji ance ana saida abinci kuma arna ke saida abincin ko da akwai nisa mai yawa sai na je na duba ko zan ga Alawiyya ko Iyami amma ko mai kama da su ban taɓa gani ba.

Cikin taimakon Allah na sake samun jarin gyaran motoci da mashina a ƙofar shagon dana kama haya nake gyarana.
Sai ga Ni na fara sayen mataccin motoci ina gyara su ina saidawa da farashi mai tsada, kafin ka ce me? Har na samu kuɗin da na sayi gidana ƙarami a Kaduna na kuma siyi mota mai kyau ba laifi ina yawon neman ɗiyata Alawiyya.

Na jima a Kaduna har Allah Ya haɗa Ni da wani Alh Abu Katsina wanda nake turama motocina da nake saye ina gyarawa yana siye.
Sosai muke kasuwanci da shi wanda shi ne yaban shawarar na koma Katsina da kasuwancina sai na fi samun alheri.
Kamar ba zan yadda ba sai da wata rana ya kirani a waya ya ce min, "Nasa anyi maka istihara an tabbatar min da cewar zaka ga Alawiyya amma fa a ƙasar Katsina sai dai ban san a wane gari bane ba ko ƙauye ne za ku haɗu ba.
Hakan yasa na shirya kayana tsab daman na biya kuɗin aikin hajji zan je sai na tsara tafiya ta jihar Katsina yadda idan na dawo zan cigaba da zama a Katsina kawai ina cigaba da neman Alawiyya.

Bayan na dawo Makkah abubuwa suka ƙara buɗewa sosai da sosai arziƙi ya zauna na zama babban attajiri sai na dinga siyen gidaje ina zuba mutane marassa ƙarfi a kyauta kafin su yi nasu.

Haka a kowace rana ana dafe min buhunnan shinkafa na bada sadaka duk don Allah Ya bayyana min ɗiyata.

Kar da ku ɗauka na manta da iyayena a'a suna raina amma dana tuna sune silar rabuwata da ahalina dai na ji na tsane su ban san komawa gunsu sai da ahalina da suka raba mu.

Haka zalika nayi alƙawarin ba zan taɓa aure ba sai na samu labarin rasuwar Fatima sannan zan sake aure amma idan ba mutuwa tai ba zan ta jiranta har ta bayyana a gareni.

A haka ne wata rana ina zaune sai ga ɗaya daga cikin yarana yake gayamin ɗaya daga cikin ma'aikatana bata lafiya ga ɗiyarta na son gani na, na ba shi damar shigowa da ita, abin godiya ga Allah sai ga Alawiyya na gani, tunda na rabu da Alawiyya bata taɓa ɓace min ba ko a fuska don haka ina ganinta na gane ita ce Alawiyya jinina ɗiyata da nake nema shekara da shekaru.
Wannan shi ne labarina cewar Daddy yana kallonsu.

Su duka su kai shiru suna jinjina lamarin rayuwar tasu baki ɗaya, Alawiyya ta dubi Jiddah tace, "Wai kam baki samu labarin inda Babanki yake ba har zuwa yanzu ba Jiddah?"
Jiddah ta taɓe bakinta tace, "Ki manta kawai Barista ya manta da Ni kamar yadda na manta da shi nima, amma ina mai addu'a Allah Ya shirya shi Yasa ya gane cewar yara na da haƙƙi kan iyayensu kamar yadda iyaye ke da haƙƙi kan yaransu." Ta ƙare maganar tana share hawayen takaici.

Mustapha sai kallonta yake yana ji a ransa cewar duk ranar da ya aureta zai mata gata zai maida ta sarauniya tabbas zai sa ta mance duk wani ɓacin ranta na baya. 
Bai taɓa tunanin akwai ranar da zai zubar ma wata mace da hawayen tausayi ba sai ga shi yana zubarwa Jiddah lokuta da dama.

Jiddah ita ce macen da yake mafarki, ita ce yake gani suna rayuwar farin ciki ita ce yake fatan ta gyara mai gidansa ta zama silar wanzuwar farin ciki a gidansa.

Bai jin zai iya ɗaga ma kowa akan auren Jiddah ya shirya ya gama komai na auren Jiddah jiran lokaci kawai yake domin bai yadda cewar akwai wanda zai iya auren Jiddah ya saka ta cikin farin ciki fiye da shi ba.

Hakan yasa yake hangen kowane namiji ba zai iya riƙe Jiddah yadda zatai farin ciki ba shi ne kawai zai iya riƙe Jiddah ta rayu cike da jin daɗi domin yasan cewa zai iya haƙura da farin cikinsa ya sa Jiddah farin ciki haka zai iya haƙura da komai indai Jiddah bata muradi to shima bai muradin koma miye.

Ta ɓangaren Dr Faisal kuwa shi ma ji yake ba wata katanga da zata iya shiga tsakaninsa da auren Jiddah, bai jin zai saken da zai rasa macen kirki kamar Jiddah mai ladabi da biyayya mai rayuwa kamar ta matan Sahabbai. Ya kalli Alawiyya gabanshi ya so faɗuwa amma sai ya dake domin bai kamata ba ace matarsa ƙanwarsa ta zama abar tsoro a gare shi ba, kamata ya yi ma ace ita ce zai fara tunkara da maganar neman auren Jiddah domin ta shige mai gaba kan yiyuwar lamarin matsayinta na babbar Aminiya kuma ƴar'uwa da suka tashi waje guda.


Barista Alawiyya kuwa hangen ta inda zata fara take kawai, shin Baban Jiddah zata fara nemowa ko mijin Jiddah? Tabbas alƙawarinta sai ya cika sai ta hukunta mahaifin Jiddah ko da Jiddah zata nuna mata rashin jin daɗinta haka sai ta hukunta Deeni ko da yaran Jiddah ba za su ɗauke ta matsayin uwa ba. Ya zama wajibi ta bazama neman mahaifin Jiddah duk duniyar da yake domin ta koya mai karatun da bai koya ba, ta ɗora shi kan hanyar da ya sauka ta gyara mai kuskurensa kamar yadda ta koma ta ɗauki fansa gun Hakimi ta hanyar banka shi kotu ta dabaibaye shi da manyan hujjojin ta kai tsaye ya amsa laifinsa na kashe matarsa Baba Hassu wanda yanzu haka yana gidan yari an yanke mai hukuncin kisa ta hanyar zama gidan yari na har abada.

Fatima kuwa tunanin ta yanzu ya zatai da Alƙali ne ya turo mata saƙon yana son ganinta kafin a koma kotu ya ƙara da gaya mata ta kwantar da hankalinta Shari'a zatai mata kyau kamar yadda take da kyau. Shin me yake nufi da kalamansa ne? Ita fa ba mutunniyar banza bace balle ya yi amfani da hakan ya cutar da ita ba, idan kuma sonta yake ita kam tayi bankwana da aure har abada, domin tana cikin tsanar maza ne kan abin da Abubakar ya yi mata bata manta ba ga zamanta da Deeni da bai goge mata ba a zuciyarta ba, ina ita ina wani aure yanzu? Me mazan su kai mata na kirki da zatai wani aure? Ai yanzu aikinta kawai da yaranta da mahaifiyarta ke gabanta bata da sauran wata damuwa yanzu sai ta wannan shari'ar ana gama ta zata tattara ta koma garinsu domin ƙwatarwa mata da dama haƙƙinsu da yara ƙanana wannan shi ne sabuwar rayuwar da zata mutu kanta.


To jama'a kun dai ji tunanin kowa.
Sai ku biyo Haupha don jin yadda za ai.

Taku a kullum Haupha ✍️