Gyaran Dokar Masarautu: An yi kira ga Gwamnatin Sokoto kar ta taɓa ikon Sarkin Musulmi

Gyaran Dokar Masarautu: An yi kira ga Gwamnatin Sokoto kar ta taɓa ikon Sarkin Musulmi

A satin da yagabata ne Gwamnatin jihar Sakkwato ta ba da bayanin za ta yi gyaran fuskan kan dokar masarautu in da ta cimma matsaya a zaman majalisar zartawa da ya gudana a fadar gwamnatin jiha.

Wannan bayanin ya haifar da cece-ku-ce a jiha abin da ya kai ga shugaban Kungiyar Kariyar Martabar Tarihi, Masarautu da Al'adun Cibiyar Daular Usmaniyya Nuraddeen Muhammad Mahe ya rubuta budaddiyar wasika ga gwamnan jiha Dakta Ahmad Aliyu Sakkwato ya ce "maigirma Gwamna ina ganin cewa an kawo gabar da yakamata ince wani abu saboda komi hurumi gare shi. Ina son in baka shawara ne akan kudurin gyaran doka na Ma'aikatar Kananan Hukumomi da Lamurran Sarakuna da Gwamnatin ka ke son karbe wasu powers daga Majalisar Mai alfarma Sarkin Musulmi zuwaga Gwamna.

 

"Maigirma Gwamna a ganina yakamata abar halas don kunya domin kuwa koda ba'ayi gyaran doka ba ai ko yanzu ma Gwamna ne keda karfin iko na cirewa da nadawa don ko yanzu munga irin canje-canjen da kayyi a inda aka cire wasu sarakuna aka yiwa wasu transfer daga ciki akwai yan majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi da Kingmakers 4 wadanda suka hada da Magajin Gari, Sarkin Kabin Yabo, Sarkin Yakin Binji da Baraden Wamakko. A yayinda wasu daga cikinsu ke zaman jiran sakamakon bincike.

 

"Maigirma Gwamna yakamata mu rinka dogon nazari akan taba wani hakki na Masarauta musamman irin ta Sakkwato domin akwai daraja da girma da take da ita fiyeda sauran wurare. Duk da cewa ku "Yan Siyasa" ke da iko kamar yadda tsarin mulki ya baku, akwai bukatar kuyi respecting traditional institution domin duk ta nan muka fito," Kalaman Nuraddeen Mahe.

 

Ya ci gaba da cewa "yakamata ace ma yanzu an kawo gabar da muke ganin ya dace aba Sarakuna wani role a cikin kundin tsarin mulkin kasa ba a cire dan wanda suke tusarrafi da shi ba. 

 

"Maigirma Gwamna ko yanzu in ka duba ba wata power da Sarkin Musulmi ke da ita wurin bayarda sarauta abin da aka barshi da shi kawai shi ne nadawa. Nadin da zai yi ne kadai zaiyi validating na cewa sarauta ta tabbata. Yakamata Gwamna ya kalli irin damar da Allah ya ba shi yayi godiya ga Allah ba tare da ya taba na Masarautar mai alfarma Sarkin Musulmi ba.

 

"Yanzu abinda jahar mu ke nema shi ne tura bukatu wadanda zasu kawo ma al'umma sauki da walwala ba canja wata doka ba. Cigaba da yin haka zai kara tabbatar da zargin da mutane ke yi na cewa akwai wata agenda tsakanin gwamnati da masarautar mai alfarma Sarkin Musulmi.

 

"Daga karshe ina kara tunatar da maigirma Gwamna cewa jahar Sakkwato ita ce cibiyar Daular Usmaniyya tana da banbanci da sauran jahohi mai girman gaske. Yakamata ace mune gaba-gaba wurin karfafa masarautar mu, tarihin mu da al'adar mu ba masu son tauye musu hakki ko rusasu ba," a cewar shugaba Nuruddeen.