Gwamnonin Nijeriya  Ba Sa Tsoron Zaɓen 'Yar Tinke---Gwamnan Jigawa 

Gwamnonin Nijeriya  Ba Sa Tsoron Zaɓen 'Yar Tinke---Gwamnan Jigawa 
Gov. Badaru

 

Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya shaidawa sashin Hausa na BBC cewar, gwamnoni, musamman na Jam'iyar APC ba sa tsoron ayi zaben ƴar tinƙe, wanda a ka fi sani da ƙato-bayan-ƙato.

 

Gwamnan ya baiyana cewar, damuwarsu ita ce yawan kuɗaɗen da za a kashe yayin gudanar da wannan zaɓen, domin a cewarsa "dole zaɓen zai ci kuɗi sosai,  saboda yayi kama da zaɓen du-gari.

 
Ya ƙara da tambayar cewa, "a ina Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai Zaman Kanta, INEC zata samo kuɗaɗen da za ta gudanar da wannan zaben?"
 
Domin, a cewar gwamnan, idan an ce ko ina za a baiwa mutane dama su yi zaɓen to dole a ɗauki ma'aikatan zaɓe kuma dole a biyasu.
Ya ce in har gwamnatin Nijeriya tana da kudaden da za ta kashe a yi wannan zaben suna goyon bayansa.
Managarciya tana hasashe kamar yadda sauran mutanen kasa ke yi cewa Gwamnonin Nijeriya ba sa goyon bayan zaben kato bayan kato wanda ake da 'yar tinke ko na kai tsaye.