Gwamnonin Arewa ta yamma sun jingine bambancin siyasa domin maganin tsaro a yankin

Gwamnonin Arewa ta yamma sun jingine bambancin siyasa domin maganin tsaro a yankin
 
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karbi bakuncin Gwamnonin Arewa maso Yamma a taron kaddamar da jami’an tsaro na jihar (CPG).
 
A  laraba ne aka gudanar da bikin yaye  sabbin jami’an tsaro da zasu tsare yankunan su (Community Protection Guards) da aka radawa sunan Askarawan Zamfara a  babban filin taro na bajakoli da ke babban birnin Gusau.
 
A wata sanarwa kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi, Kaduna, Kano, Katsina da Sakkwato sun halarci bikin yaye jami’an.
 
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Zamfara tana amfani da hanyoyi da dama don magance matsalolin tsaro a yanzu da kuma nan gaba.
 
“A shekarar da ta gabata, Gwamna Dauda Lawal ya amince da daukar masu gadi 5,200 a fadin kananan hukumomi (14) dake jihar. A yau, an yaye 2,645 daga daga masu tsaron al’ummar a matsayin rukunin farko. "
 
A nasa jawabin a wajen bikin yaye jami’an, Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ta fara aiki mai wuyar gaske tare da kudirin yin garambawul a hankali a dukkan sassan tattalin arzikin jihar domin samar da hayyaci da kuma bunkasa ci gaba.
 
“Yayin da muke yin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce, ba zamu cimma burin mu ba muddin ba a magance matsalar rashin tsaro ba wadda tazama babbar ƙalubale a garemu.
 
“Wannan dalilin yasa muka yanke shawarar kafa jami’an kariyar Jama’a, wanda aka fi sani da Askarawa. Kwamitin gudanar da aikin ya shiga lungu da sako wurin zakulo jajirtattun jami’an da zasuyi wannan aiki daga kanananhukumomi (14) na jihar.
 
“Mun yi imanin cewa galibin kalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na jiha sun samo asali ne daga tsananin sakaci wajen ciyar da manufofin jama’a don biyan bukatun zamantakewar al’ummar mu. Ba za mu taba yin wasa da hakkin al’ummar jiharmu da yake kanmu duba da kuri’unsu da suka jefa muna a zaben da ya gabata a watan Maris 2023.
 
“Saboda haka, a yau rukunin farko na jami’an tsaron al’umma, 2,645, ne aka yaye. Wadannan ma’aikata matasa, masu kuzari da ƙwazo sun samu ingantaccen horo, fahimtar ƙa’idojin aiki, da dai sauransu, wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na haɗin gwiwa, taimako da aiki tare da hukumomin tsaro don kare al’ummominmu. ”
 
A nasa jawabin, Dr Dikko Radda, Gwamnan jihar Katsina kuma shugaban gwamnonin arewa maso yamma, ya jaddada matsayarsu ta hadin gwiwa na kin tattaunawar sulhu da ‘yan fashi.
 
“Mun hallara a nan ne a yau da manufa guda: mu hada kai don yakar ‘yan fashi da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma. Ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, mun kuduri aniyar cewa ba za mu taba tattaunawa da ‘yan fashi ba," kalamansa.